Dubban Miliyoyin Masoya Annabi Muhammadu SAW A Garin Gombe Sun Gudanar Da Zagayen Takutaha 2024

GOMBE TAKUTAHA 2024

 

Al’ummar Musulmi Sun Gudanar Da Gagarumin Taron Zagayen Takutaha A Kofar Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar Na III Don Nuna Murna Da Ranar Suna Don Samuwar Fiyayyen Halitta SAW.

 

Taron Zagayen Takutaha Wanda Shine Karo Na Shida Wanda Mai Martaba Sarkin Gombe Yake Shiryawa Tare Da Kungiya Shu’ara’ul Islam Ta Jihar Gombe Wanda Alhaji Barhama Adamu Damanda Yake Shugabanta.

 

Mutanen Sun Samu Halarta Tare Da Nuna Farin Cikin Su Da Wannan Taro, Tare Da fatan Alkhairi, Allah Ya Maimata Mana.

 

Hakimai Da Wasu Rike Da Sarautun Gargajiya Sun Samu Halarta Tare Da Manyan Malamai, Limamai, Da Jami’an Gwamnati Harma Da Jami’an Tsaro.

 

Islamiyoyi Da Sha’irai Da Masoya Sune Suka Gudanar Da Zagayen Kamar Yadda Aka Saba Duk Shekara, An Gabatar Da Jawabai Da Nasihohi A Yayin Taron.

 

ALLAH ya kara mana soyayyan Manzon Allah SAW, ya maimaita mana albarkan Annabi Muhammadu ﷺ. Amiin

 

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button