Fuskokin Wasu Daga Cikin Wadanda Suka Rasu a Ruftowar Ginin Babban Masallacin Garin Zaria jihar Kaduna.
Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un:
Fuskokin wasu daga cikin waɗanda suka rasu a ruftowar ginin babban Masallacin garin Zaria jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne bayan kammala sallar juma’a inda babban Linta biyu a tsakiyar babban Masallacin suka balle suka fado kan masu Sallar La’sar.
Mutane da dama sun rasu har zuwa yanzu ana cigaba da tsakulo mutanen da ginin ya danne, kamar yadda wata majiya a bayyana mana dake Zaria.
Yanzu cikin dare aka gudanar da jana’izar mutane 8 cikin mutum 10 da suka rasu a babban Masallacin Zaria, bayan ginin masallacin ya fado musu, suna tsakiya da yin Sallar la’asar.
Dukkan su suna daga cikin wa ‘yanda Allah ya karbi rayuwarsu, a babban masallacin garin Zariya, bayan ginin masallacin ya fado musu, suna tsakiya da yin Sallar la’asar.
Na farkon sunan su Malam Adamu Idris, na biyun sunanshi Hussaini Hussain Zakariya, na ukun sunanshi Shehu Yahya.
Muna musu Addu’ar Allah ya jikansu da Rahama da sauran wa ‘yanda suka rasu.
Allah ya jikan wa ‘yanda suka rasu, Allah ya bawa wa ‘yanda suka jikkata lafiya. Amiin