Ga Kadan Daga Cikin Abinda Ya Fada A Lokacin Ziyarar Da Yakai Kasar Palestine Shekara 1966.

Sheikh Ibrahim Inyass (RA) A Cikin Ziyarsa A Masallacin Kudus Na Falasdin A Shekarar 1966. Ga Kadan Daga Cikin Abinda Ya Fada A Lokacin Ziyarar:

 

Na sami alfarmar yin Sallar Juma’a a cikin masallacin Aqsa (Kudus) da Wazifa mai tsarki a karkashin Dutsen Sakhrah mai albarka, daga in da Manzonmu (SAW) ya tafi Mi’iraji.

 

Ni da kaina ina kallon bala’in Falastin (Palestine 🇵🇸) a cikin zurfin rai na. Kudus tana wakiltar Zuciyar Al’ummar Musulmi, a gareni.

 

Kudus tana bukatar mazaje masu tsarkin zuciya kwatankwacin Irinta Sayyidna Umar (RA), ba ’yan siyasa masu son duniya ba.

 

Za a ci gaba da Jihadi a kewayen Baytul Maqdis har zuwa ranar sakamako, kamar yadda ya tabbata a Hadisi.

Share

Back to top button