GAIBU Na Nufin Al’amurran Da Suke a ‘Boye a Zamanin Baya Ko Na Yanzu, Ko Kuma Abubuwan Da Za Su Zo a Gaba.
Menene GAIBU:
GAIBU Na Nufin Al’amurran Da Suke a ‘Boye a Zamanin Baya Ko Na Yanzu, Ko Kuma Abubuwan Da Za Su Zo a Gaba.
KU ƊIYAN ‘ƘUNGIYA KU KAN BUGI ‘ƘIRJI KU CE; ANNABI(S.A.W) BAI SAN GAIBU BA, DUK DA WAHAYIN DA ALLAH KE YI MASA NA ABIN DA BABU WANDA YA SANI, WANI LOKACI KUKAN CE AI TUNDA AN SANAR DA ANNABI(S.A.W) ABIN YA ZAMA BA GAIBU BA, A TUNANINKU WAI GAIBU SAI ABIN DA ALLAH KAƊAI YA SANI.
To Gaskiya Wannan ‘Koƙarin ‘Kasƙantar Da ANNABI(S.A.W) Ne Da ‘Koƙarin Daidaita ‘Kadarinsa Da Game-Garin Jama’a.
A Wurin ALLAH(S.W.T) Babu Gaibu, Domin Lokaci Da Wuri Basu Da Tasiri Akan ALLAH – Ma’ana Da Ɗazu Da Yanzu Da In An Jima Duk Abu ‘Daya Ne a Wurin ALLAH. In Baka Gane Ba, a Ilimin ALLAH Yanzu Aka Haifeka, Yanzu Kake Rayuwa, Yanzu Ka Mutu, Kuma Yanzu Ake Yi Maka Hisabi.
A TAƘAICE ALLAH YANA GANIN KOMAI A LOKACI GUDA(GANI IRIN WANDA YAYI DAI-DAI DA GIRMANSA), SANNAN YA SAN KOMAI FARKONSA ZUWA ƘARSHENSA. Don Haka ALLAH Baya Da Gaibu.
Duk Inda Ka Ji ALLAH Yayi Zancen Gaibu a Alƙur’ani, To Ya ‘Kirata Gaibu Ne Don Mu Bayi Wasunmu, Ko Dukkanmu Bamu San Abin Ba. WURINMU YAKE GAIBU, TO SAI ALLAH YA ‘KIRA ABIN GAIBU DON MU GANE INDA AKA NUFA TUN DA SAƘON NAMU NE. Don Haka Abin Da Ake ‘Kira Gaibu, Shi Ne Abin Da Bayi Irin Ni Da Kai, Ko Dukkan Halitta Basu Sani Ba, Ko Ya Faku Ga Ilimi Da Idanunsu.
Kamar Yanda ALLAH Ke Kiran Wani Abu Gaibu In Wasu Bayi Ko Dukkan Bayi Basu San Shi Ba, To Haka Kuma Wani Abu Zai Iya Zama Gaibu Wurin Wasu Bayi a Yayin Da Yake Ba Gaibu Ba a Wurin Wasu.
ALLAH Ya ‘Kara Tsare Mana Imaninmu, Ya ‘Kara Mana Ladabi Ga Janibin ANNABINMU (S.A.W) Ameeen.
Daga: Othman Muhammad