GAMSASSUN HUJJOJI NA HADISI MASU NUNA CEWA IYAYEN ANNABI (SAW) ‘YAN ALJANNA NE.
DALILAI NA HADISI MASU NUNA CEWA IYAYEN ANNABI (SAW) ‘YAN ALJANNA NE.
Sheikh Halliru Abdullahi Maraya Kaduna.
Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) da Ya ba mu dama , a jiya , muka gabatar da wasu daga cikin dalilai na hankali masu nuna cewa iyayen Manzon Allah (SAW) ba ‘yan wuta ba ne . Allah (SWT) Ya kara masu (AS) rahama da yarda. Insha’Allah, yau, zamu kawo wasu dalilai na Hadisin Manzon Allah (SAW) masu nuna haka Allah (SWT) Ya kara wa ManzonSa (SAW) matsayi da alfarma. Akwai dalilai na Hadisin Manzon Allah (SAW) da suke nuna cewa iyayensa (AS) muminai ne , ‘yan Aljanna . Daga ciki akwai:
i. Waathilah Ibnu Asqa’i (RA) yace: Manzon Allah (SAW) ya ce “Lallai Allah Ya zabi Ismaa’iil (AS) daga cikin ‘ya’yan Ibraahiim (AS) kuma Ya zabi ‘ya’yan Kinaanah daga cikin ‘ya’yan Isma’iil (AS), kuma Ya zabi Quraysh daga cikin ‘ya’yan Kinaanah , kuma Ya zabi ‘ya’yan Haashim daga cikin Quraysh , sannan (daga karshe) Ya zabe ni daga cikin ‘ya’yan Haashim .”Manazarta : Sahiihu Muslim .
ABUN DA HADISIN KE NUNAWA:
Wannan Hadisi yana nuna cewa acikin kowace Jama’a , tun daga Annabi Ibraahiim (AS) har zuwa lokacin haihuwar Manzon Allah (SAW) , Allah (SWT) Yana zaben mutane ne mafifita a wurinSa (SWT), sannan Ya sa Manzon Allah (SAW) a tsatsonsu. A takaice, mai lafiyayyen hankali zai fahimta daga wannan Hadisi cewa iyayen Manzon Allah (SAW), tun daga Annabi Ibraahiim (AS) zuwa iyayensa na haihuwa, zababbu ne a wurin Allah (SWT). Kafirai kuwa ba zababbu ba ne a wurin Allah (SWT) . Saboda haka, Hadisin ya nuna cewa Abdul-Laahi (AS) da Aaminatu (AS) , iyayen Manzon Allah (SAW) , zababbu ne a wurin Allah (SWT) ba ‘yan wuta ba.
ii. Sayyidunaa ‘Aliyyu (RA) ya ce : Manzon Allah (SAW) ya ce : ” An haife ni ne ta hanyar aure , ba a fitar da ni ba ta tsatson mazinaci tun daga Aadam (AS) har zuwa lokacin da mahaifina da mahaifiyata suka haife ni .”Manazarta : Imam At- Tabaraaniyyu , Mu’jamul-awsad.
ABUNDA HADISIN KE NUNAWA:
Wannan Hadisi na nuna cewa iyayen Manzon Allah (SAW) , Abdul-Laahi da Aaminatu (AS) , ko zina basu taba yi ba , balle kafirci.
Manzon Allah (SAW) na alfahari da cewa iyayensa (AS) ko zina basu taba yi ba . Wato cikakkun mutane ne na kwarai. Mu sani , kafirci shi ne sabon Allah (SWT) mafi muni da girma. Iyayensa (AS) ba kafirai ba ne , da kafirai ne , da bai yi alfahari da cewa ko zina basu taba yi ba.
Domin da kafirai ne , da kenan sun aikata laifin da ya fi zina girma sosai . Saboda haka , da bai yi alfahari ba da rashin yin zinarsu. Misali: Mutum ne iyayensa ba sa shan taba , amma suna shan koken (Cocaine) , dan Allah zai iya alfahari saboda cewa iyayensa ba sa shan taba ? A nan zan tsaya yau. In sha’Allah, gobe ko jibi , zan yi magana a game da ainihin mahaifin Annabi Ibraahiim (AS) , wato daya daga cikin kakannin Manzon Allah (SAW) . In sha’Allah , zamu ji waye hakikanin mahaifinsa.
Daga baya kuma , in sha’Allah , sai mu je kotun koli , wato Alqur’ani Mai girma , a game da cewa iyayen Manzon Allah (SAW) ba yan wuta ba ne kamar yadda wasu ke tallatawa . Allah Ya kiyaye ! In sha’Allah , daga karshe , sai mu rufe da yin magana a game da hujjojin da masu wannan mummunar maganar suke amfani da su domin a yarda da wannan magana tasu mai munin gaske . Allah (SWT) Ya kara wa Manzon Allah (SAW) , alayensa (AS) , da
sahabbansa (RA) matsayi da yarda. Mu kuma , Allah (SWT) Ya kara mana soyayyarsu.
Allah Ya kara wa kasarmu, Nijeriya , arziki da zaman lafiya. Duk wadannan, Allah Ya amsa mana saboda alfarmar Manzon Allah (SAW). Amiiiin Yaa ALLAH