GENOTYPE A MUSULUNCI TARE DA BINCIKEN MASANA KASHI NA DAYA (1)

GENOTYPE A MUSULUNCI (1)

*

Ilimin kimiyya abune karɓaɓɓe a musulunci sai dai hanyoyin samu ko tabbatar da ilimin ne ya kan iya cin karo da koyarwar musulunci, kafin in shiga bayani akan genotype, yana da kyau mu san wannan

 

WAYE MUTUM?

A wurin duk cikakken musulmi, Annabi Adam ne mutum na farko kuma uban dukkan mutane, Sannan Allah ya halicce shi ne a sama daga “yumɓu/laka”, ya shigar dashi aljanna sannan ya saukar dashi duniya shi da matar sa suka haifi yara. Amma a wurin kimiyar turawa, mutum shine duk wani halitta da yake a jinsin “Homo” (kalmar Latin dake nufin mutum) kuma jinsin homo na farko shine “homo habilis” wayanda suka rayu miliyoyin shekaru kafin zuwan Annabi Adam A.S.

 

A wurin su, mutum na farko (homo habilis) kama yake da biri, haka yayi ta samun kyautatuwan halittar sa har ya dawo suffar mutanen yanzu (modern human) wayanda suke kira “homo sapien”.

 

Turawan sun yi bincike na DNA ne akan ragowar jikin halittun da suka tono/samo wayanda suka rayu miliyoyin shekaru a duniyar nan kafin saukowar Annabi Adam shiyasa suka fadi haka. Tabbas sun nufo gaskiya amma cikin duhu, domin basu san cewa Allah ya aiko mala’iku duniya suka dibo mai ƙasa mabanbanta domin kwaɓa halittar jikin Annabi Adam ba, shiyasa ba abin mamaki bane don sun samu DNA din halittun da suka fara zama a duniya kafin zuwan Annabi Adam a jikin mutanen yanzu.

 

Duk wanda ya fahimci wannan, zai gane ba za a samu cikakken bayanin halittar ɗan adam a wurin bature ba, dole sai an waiwaya musulunci.

 

MENENE GENOTYPE?

Genotype yana nufin “Dandali ko dunkulen sinadarai/kwayoyin da suka samar da halitta (organism)”, sun ƙunshi abubuwa kamar haka:

 

A) “CELL” shine mafi ƙanƙantar ƙwayar halitta dake iya rayuwa da kanshi kuma shine yake haduwa ya samar da halitta mai rai (living organism). Cell yana da sashi uku, sune Membrane, nucleus da cytoplasm.

 

B) “GENE” shine asalin sashi (basic unit) na gado (heredity) wanda yake zuwa ga yara daga iyayen su, wato gadon suffar jiki da halayya. Shi wannan “Gene” din ya kunshi na’ukan DNA (Deoxyribonucleic acid) wayanda aka jera su daya bayan daya.

 

C) Chromosomes shine sashin da aka jera Gene, kuma yana cikin sashin NUCLEUS na jikin kwayar halitta (cell).

 

Akwai kwayoyin Gene aƙalla guda 955 a cikin kowani Chromosome ɗaya, A cikin Nucleus din kowani ƙwayar halitta (cell) akwai chromosomes guda 23.

 

Genotype shi yake haifar da “Phenotype” wanda yake nufin Halayya/dabi’a ko wani abu wanda halitta (organism) ta kunsa ko ta nuna.

 

Da wannan ilimin ne ake iya gane wane kaza genotype din shi kaza ne, wane kaza ma genotype din shi kaza ne, sannan da yiwuwar su haifi yara iri kaza.

 

A RUBUTU NA GABA ZA MU KAWO YADDA SUKE A MUSULUNCI DA KUMA YADDA ZA A TSALLAKE MATSALAR RASHIN DACEWAR SU INSHA ALLAH.

 

✍️ Sidi Sadauki

Back to top button