RAYUWAR KABARI, DA TAMBAYOYI, DA AZABA KO NI’IMA A CIKINSA A MUSULUNCI.. (01)
RAYUWAR KABARI, DA TAMBAYOYI, DA AZABA KO NI’IMA A CIKINSA A MUSULUNCI.. (01)
GABATARWA:
BismilLah, was Salatu was Salamu ala RasulilLahi, wa ala Alihi wa Sahbihi waman walahu, Bayan haka:
Lallai kusanto wa al’umma da ilimi, da sauƙaƙa masu shi ta yanda kowa zai fahimta, shi ne babban makamin da zai rusa duk wani shirme, da soki- burutsu da masu dakon shubuha suke yaɗawa a cikin zukatan matasa masu so da shauƙin addinin Musulunci, da neman sanin ilmominsa, hakan kuma shi ne zai cigaba da zama tamkar wata katanga, da za ta kare su daga bin masu tallar ɓata da sunan binciken gaskiya, ko wani take mai kama da haka, alhalin kuwa abin ba haka ba ne.
A daidai wannan lokaci da matasa suke ƙishirwan so da shauƙin addini, da neman saninsa, domin su ƙara riƙo da shiriyar Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), a daidai wannan lokacin ne kuma wasu suke toshe masu hanya, suke baba- kere domin su hana su bin turba ta ƙwarai, ba ma su tsaya a haka ba, sai suka fara ƙawata wa waɗannan tsarkakan matasa son zuciyarsu, suna gabatar masu da shi a matsayin shi ne ainihin addini, da ma yaya kake tunanin mutumin da yake bauta wa son zuciyarsa zai yi idan ya sami ire- iren waɗannan tsarkakan zukata da suka rasa waɗanda za su yi riƙo da hannayensu?!..
Saboda sauke wajibcin kashe gobara a lokacin da take ɓarna ne ya sanya ni shigowa wannan fagen, ba wai domin iyawa, ko ƙwarewa ba, ina mai fatan samun dacewa da ikhlasi, ikhlasin da zai wadatar da ni daga kowane irin yabo, ko suka.. Kaman yanda nake kira ga ‘yan uwa malamai, da abokan karatu akan kada su manta da abin da suka saba, na tsokaci, da gyara akan abubuwan da suka ga sun saɓa lamba a cikin wannan rubutun, Allah ya taimake mu baki ɗaya, ya kuma saka wa kowa da alhairi.
Da farko dai, yana da kyau mu san cewa malamai sun karkasa ilimin Tauhidi zuwa rukuni guda uku:
Rukuni na farko sun kira shi da suna: “al- Ilahiyyat”, wato a wannan rukuni an taɓo duk wani abu da ya zama dole a sani game da Allah Maɗaukakin Sarki, tun daga samuwarsa, zuwa sifofinsa na kamala, da kuma abubuwa da ya tsarkaka ga barinsu.
Rukuni na biyu kuma sun kira shi da suna “al- Nubuwat”, wato a wannan rukuni kuma abubuwan da suke da jiɓi da Annabawa da Manzanni masu tsira da aminci ne ake taɓowa, fara tun daga sifofin da suka wajaba a danganta su da su, da waɗanda ba su halatta a danganta su da su ba. Duka waɗannan rukunnai guda biyu abubuwa ne da hankali zai iya riska cikin sauƙi, saboda irin yanda Ubangiji ya halicce shi, ya kuma tanadar masa da hanyoyin da za su tallafa masa wajen riskarsu.
Rukuni na uku shi ne ake kira da “al- Sam’iyyat”, ko “al- Ghaibiyyat”, shi wannan rukuni yana zuwa ne bayan waɗancan rukunnai biyu da muka ambata, wato idan hankali ya jagoranci ɗan Adam a fagen abubuwan da suka shafi Allah Ubangiji, da fagen Annabawa da Manzanni, ya sami cikakken yaƙini game da tabbatuwa gami da samuwarsu, a nan kuma zai sallama ɗan Adam ne zuwa ga matakin da ya fi ƙarfin riskarsa, sai dai duk da haka, zai sallama shi a hannun da ya riga ya gama samun tabbacin cewa hannu ne na gari, wato zuwa ga wahayi, domin shi kuma ya cigaba da jagorantar ɗan Adam zuwa fagen imani da abubuwan da suke ghaibi ne a haƙƙin ɗan Adam, Allah ne kawai ya san su, irin su: alamun tashin alƙiyama, da hisabi, da mizani, da siraɗi, da aljanna, da wuta da sauransu.
Saboda haka, ya kamata mu san cewa maudhu’in da za mu yi magana akan sa a wannan karon shi ne: “Rayuwar Kabari, da Tambayoyi, da Azaba ko Ni’ima a Cikinsa”, yana cikin wannan rukuni na uku ne, wato rukunin da hankali ba shi da ta cewa, saboda ba shi da daman da zai iya hararo wannan fagen, domin ba su riga sun faru ba tukunna, ba kuma shi da wani abu da ya yi kama da su balle ya yi ƙiyasinsu akansa, abin da zai iya yi kawai shi ne ya sallama ɗan Adam a amintaccen hannu, wato wahayi, shi ya sanya ake kira wannan rukuni da “al- Sam’iyyat” wato abubuwa da jinsu ɗan Adam zai yi ta hanyar Nassoshin Shari’a da Hadisan Annabawa ya yi imani, ko “al- Ghaibiyyat”, wato abubuwan da suka ɓuya ga barin hankalin ɗan Adam.
Saleh Kaura