Tarihin Fatima Yar Sheikh Ibrahim Inyass Na Farko A Duniya.

FATIMA YAR GAUSIN ZAMANI (YA FATU)

 

Ita ce babbar diyar Shehul Islam Alhaji Ibrahim Niasse Allah ya ƙara yarda a gare shi, kuma matar cikamakin Halifofi Imamu Ali Cisse, kuma mahaifiyar Imamul Faira Sheikh Hassan Cisse Allah ya ƙara yarda a gare shi..

 

Da wuya samun kamar ta domin itace yar Gausi, matar Qutib kuma Uwar Qutib.

 

An tabbatar da cewa tun tana da ƙananan shekaru take karantar da Alkur’ani, kuma sannan tana yin salla a jama’i sau biyar a rana a tsawon shekaru a masallacin mahaifinta sannan ta rika tafiya Makkah, Madina da Fez.

 

An ruwaito cewa a farkon shekarun aurenta ta samu yawaitar zubewar ciki. Don haka a lokacin da take ɗauke da cikin Imamu Hassan Allah ya ƙara yarda a gare shi, sai ta roƙi Maulana Shehul Islam Allah ya ƙara yarda a gare shi, ya yi mata addu’a ta musamman domin neman tsira ga wannan abin haihuwa ya zo duniya.

 

Shehu Allah ya ƙara yarda a gare shi, ya yi mata addu’a sannan ya bata wani abu mai tsarkin gaske ya ce mata idan an zo haihuwar a haifi yaron a kan sa.

 

Cikin ikon Allah an haifi jaririn cikin ƙoshin lafiya. Da ya ke ya zo da sirri mai girma tun haihuwarsa, kuma gashi ya kasance dan FATIMA da ALI, sai Shehu ya sawa jaririn suna HASSAN, kuma ya yi addu’ar Allah ya yi masa arzikin gadon sirrin Imam Hassan Ibn Ali Amincin Allah ya ƙara tabbata a gare shi

 

Daga cikin ‘ƴaƴanta akwai Malamanmu Sheikh Tijjani Cisse da kuma Sheikh Mahy Cisse.

 

Sheikh Tijjani Cisse

 

A Lokacin da aka haifi Sheikh Tijjani, nan take Shehu ya sanya masa suna “Sheikh Ahmed al-Tijani”. Mahaifinsa Imamu Ali Cisse, ya yi wata addu’a a rubuce : “Ina rokon Allah mai girma ya zamo ga wannan abin haihuwa ya kasance cikakken magajin Shehu Tijjani”.

 

An rawaito daga Sheikh Hassan Cisse ya ce a lokacin ya ce mahaifiyarmu Yafatu Niasse tana da ciki na Shehu Mahy ta yi mafarkin shugaba Sallallahu alaihi Wa sallama, a cikin mafarkin ya umurce ta da ta sa wa yaron da zata haifa suna “Muhammad al-Mahy”. Ta boye mafarkin ga kowa. Lokacin da aka haifi jaririn kuma aka kai shi wurin Shehu Ibrahim domin ya ba da suna. Kai tsaye ya sanyawa yaron suna, “Muhammad al-Mahy.” kuma ya yi wata magana mai girman gaske.

 

Allah ya ba mu albarkar ta albarkarci Imamu Hassan Cisse…

 

~Mujaheed Magaji Muhammad

Share

Back to top button