TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA TAKWAS (8)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 8

 

AUREN ANNABI (SAW) DA SAYYADA KHADIJA (RTA)

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Bayan Dawowar Annabi Muhammad (SAW) Makka daga Kasuwanci da yaje garin Sham, ganin ribar da aka samu Wanda ba’a taba samu bah, dakuma gaskiya da Amanarsa (SAW), Sayyada Khadijatul Kubra ta nemi Annabi Muhammad (SAW) da ya Aureta. Wannan Lokacin Sayyada Khadijatul Kubra nada Shekaru 40 shikuma Annabi Muhammad (SAW) nada Shekaru 25.

 

Annabi Muhammad (SAW) ya amince yakuma Aureta. Ta zauna tare da Annabin Rahama (SAW) cikin ladabi da biyayya, tayiwa Addinin Musulunci hidima irin wacce ba’a taba samun Mace da tayi irinta bah. Bata taba batawa Annabi Muhammad (SAW) Rai ba.

 

Yayin zamansu da Annabin Rahama (SAW), itace Matarsa ta Farko kuma Bai Auri wata bah sai bayan Rasuwarta. Sayyida Khadijatul Kubra ita ta haifi ‘ya’yan Annabi (SAW) duka BANDA Ibrahim.

 

Ta haifi Maza 2 Mata 4 kamar haka: Abdullahi, Alqasim, Mata sune: Fadimatu, Rukiyyatu, Zainabu. Ummu-Kulsoom. dukkanin su sun rasu kafin Wafatin Annabi Muhammad (SAW) BANDA Sayyada Fadima (AS) itace uwar jikokin Annabi Muhammad (SAW) da suka wanzu a duniya tun daga wancan lokacin har yanzu.

 

Allah ya bamu Albarkacinsu bijahi Nabiyina Muhammad (SAW). Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Back to top button