TARIHIN SAYYADINA ALI ƊAN ABU ƊALIB RALIYALLAHU ANHU (Part 2) DAGA TASKAR UMAR CHOBBE
TARIHIN SAYYADINA ALI ƊAN ABU ƊALIB RALIYALLAHU ANHU (Part 2)
DAGA TASKAR UMAR CHOBBE
Ali ya wakilci ANNABI S.A.W a wajen isar da saƙon Suratut Taubah zuwa ga kafiran Makka.
Ya kuma jene a ƙarƙashin jagorancin Sayyiduna Abubakar. Matsayin Ali a zamanin Khalifofi Ali yayi mubaya’a ga Abubakar tun da farko kamar yadda ya gabata a baya.
Amma bai lizimci fadar Sarkin Musulmi Abubakar ba sai bayan rasuwar uwar gidansa Fatimah, wadda ya kasance yana jinyarta tsawon watanni ukku ko kuma shida.
Ya halarci yaƙin da Abubakar yayi da murtaddai (waɗanda suka fita Musulunci bayan rasuwar Manzon Allah) da Annabawan ƙarya, da kuma waɗanda suka ce ba sauran bada Zakka tun daga wafatin ANNABI S.A.W.
A wurin yaƙar musailamatu ne wanda Khalid ɗan Walid ya jagoranta a zamanin Abubakar, Ali ya samu gajiyar matarsa khaulatu ɗiyar Ja’afar ‘yar ƙabilar Banu Hanafi, wadda ta haifa masa Muhammad Al’Akbar, wanda aka fi sani da Ibnul Hanafiyyah.
A zamanin Sarkin Musulmi Umar kuwa, Ali ya karɓi muƙamin alƙalanci, ya kuma yi gwamna a Madina a lokuta da dama. .
Daga baya kuma, surukuta ta shiga tsakaninsa da Sarki Umar ɗan Khaɗɗabi a lokacin da ‘yarsa, Ummu Kulsum, wadda Nana Fatima ta rasu ta barta tana ƙarama ta soma girma,
Sai Sayyiduna Umar ya yi sha’awar aurenta. Ali kuwa bai yi wata wata ba ya ɗaura masa aure da ita. Wannan karimci na Ali ya ƙarfafa danƙon zumunci da ƙauna a tsakaninsa da Sarki mai ci a wannan lokaci, wanda ya bayyana cewa, ba ya da fata kamar ya haɗa zuri’a da ANNABI S.A.W abin da bai tabbata ba a surukutarsa ta farko da ANNABI S.A.W, domin kuwa ‘yarsa Hafsah ba ta haifu da ANNABI S.A.W ɗin ba.
Wannan gurin nasa kuwa ya cika domin sharifiya Ummu Kulsum ta haifa masa ‘ya’ya guda biyu, namiji da mace waɗanda ya sa ma su suna Zaidu da Ruƙayyah.
A lokacin rasuwarsa, Umar ya kafa wani kwamiti na mutum shida waɗanda ya ɗora ma su alhakin zaɓen sabon Sarki daga cikinsu.
Ali yana daga cikin membobin wannan kwamiti. Ga dukkan alamu Umar ya yi sha’awar a na ɗa Ali, amma tsentseninsa da mu ka sani bai bar shi ya ayyana shi ba, wataƙila saboda surukutar da ke tsakaninsu, sai ya bar Musulmi su zaɓa da kansu, kuma a cikin ikon Allah zaɓin bai faɗa a kan Ali ba a wannan lokaci.
Ba za mu yi mamakin Umar ya yi sha’awar Ali ya gade shi ba domin sun fi kama da juna a ɗabi’unsu da tsarin rayuwarsu kamar yadda Usman ya fi kama da Abubakar a wajen sanyin halinsa da jin kunyarsa.
Da aka zaɓi Usman kuwa, Ali shine mutum na farko da yayi masa mubaya’a kamar yadda mu ka gani a baya.
Ya kasance a matsayin wazirinsa mai ba shi shawara ko da yaushe kamar yadda yake yi a zamanin Umar.
Mun kuma riga mun ji irin gudunmawar da Sayyiduna Ali ya bayar wajen kariyar Usman kafin Allah ya ƙaddari aukuwar abin da ya alƙawarta na shahadarsa a hannun ‘yan tawaye, mutanen Iraƙi.
Ali ya zama Sarkin Musulmi Bayan da ajali ya cika da Sarkin Musulmi Usman ɗan Affan, al’amurra duk sun rikice a birnin Madina.
Ga shi kuma ba’a dawo daga aikin hajji ba wanda Sahabbai da dama suna can, sai ‘yan tawaye suka fara tunanin hanyar da zata fisshe su.
Abu na farko da su kayi tunani a kansa kuwa shine, su taka rawa wajen naɗa khalifa na gaba.
A kan haka sun zagaya wurin Ali da Ɗalhah da Zubairu da Ibnu Umar, amma duka sai suka yi biris da su, ko wanensu yaƙi amincewa da ya karɓi mubaya’arsu domin ba su ne ya kamata su yi wannan ba.
Haka dai al’amari ya dagule ma su, suka rasa wanda zai fidda su daga wannan rami da suka auka, ga kuma alhazzai suna kan hanya sun kusa isowa Madina, sai su kayi barazanar kashe dukkan waɗanda suka nema da wannan al’amari suka ƙiya masu.
Allah ya bamu Albarkacin dukkan Sahabban ANNABI S.A.W. Amiiiin Yaa ALLAH