Yan’Darikar Tijjaniyya Sun Taimakawa Majinyata Da Kuɗin Sayan Magani Don Murnan Mauludi.

ALHAMDULILLAHI QAFILATUL MAHABBA AKKO BRANCH JIYA TA SAMU GABATAR DA MAULIDINTA A GENERAL HOSPITAL KUMO.

 

Jiya jumma’a Qafilatul mahabbah Akko Branch ta ziyarci marasa Dake jiya a Asibitin General kumo Dan gaishesu Tareda Basu Taimako Dan murnan samun Manzon Allah saw.

 

Alhamdulillahi Dukkan majiyyata Dake jinya a Asibitin sun Sami wani Abu daga foundation din .

 

Jagororin Asibitin da majinyata sun nuna Farin chikin su sosai Bisa wannan Aikin na Qafila a bayanin Daya daga jagororin Dr Ahmad ya bayyana Farin chikin sa wadda yace asaninsa irin hakan Bata faru ba Sai yanxu Kuma a lokachin da ake bukatar hakan.

Sheik Aliyu Muhammad Tukur kumo na daga cikin wadda suka dafawa lamarin Dan Ganin Tabbatuwarsa .

 

A bayaninsa yace irin Qafila ake bukata masu nemowa su bayar ba Akasin haka ba.

 

Qafila Tana Mika sakon godiya ga Dukkan wadda suka Tsaya Dan Ganin anyi Aikin lfy angama.

 

Allah Mai maitamana Happy maulud ❤️.

Shafi’u Usman JT ✍️

Qafilatul Akko Branch media.

Share

Back to top button