FATWA

  • TA’ALIKI AKAN MAGAGGANUN MANYAN MALAMAI TARE DA SAYYADI UMAR CHOBBE (Kashi Na 2 )

    TA’ALIKI AKAN MAGAGGANUN MANYAN MALAMAI TARE DA SAYYADI UMAR CHOBBE (Kashi Na 2 ),

     

    PROF IBRAHIM MAQARI YANA CEWA:

     

    Adai Duba Littafin Da Kyau Tukun Kafin Ace Wai ANNABI S.A.W Bai San Gaibu Ba.

     

    Prof. Ibrahim Maqary Yace idan Mutum Yace Maka ANNABI S.A.W Bai San Gaibu ba, Kar Kace Masa Wallahi Tallahi ANNABI S.A.W Yasan Gaibu bazaku Gahimci junaba.

     

    Abunda Zakayi sai ka Tambayeshi Menene Gaibu?

     

    •Idan mai ilimi ne zai ce maka Allah Qaibu ne

     

    Sai katambayeshi “toh Allah ne ANNABIN bai sani ba??

     

    •Zai sake ce maka mala’iku qaibu ne ,

     

    sai kace masa ai “Mala’ikun yan aiken sa ne. Ai aiken su ya keyi S.A.W

     

    Ba ANNABI S.A.W ba, wanda ma ya zauna kusa dashi sai ya gansu. Su Mala’ikun

     

    •Zai sake ce maka Aljanna da wuta Qaibu ne

     

    Sai kace masa ai Ana zaune a duniya Manzon Allah ke zuwa ya dawo har yace yaga wane kaza acikin wuta kuma yaga wane kaza acikin aljannah.

     

    Ana zaune zai ce ga Aljanna ga wuta a gabana ku kuna ganin bango shi yana ganin Aljanna.

     

    •Zai sake ce maka abunda zai faru nan gaba Qaibu ne!

     

    Sai kace masa a tsayuwa daya ANNABIN ya bada labarin abunda zai faru har tashin Alqiyama

     

    “KANA FEENA RASULULLAHI S .A .W MAQAMAN FAMA TARAKA SHA’IN TAKUUNU FI MAQAMA MIHI ZALIKA ILA QIYAMISSA’ATI ILLAH HADDASANA BIHI.

     

    ALLAH YA KARAWA PROFESSOR LAFIYA DA FAHIMTA BIJAHI S.A.W. AMEEEEEN

  • TA’ALIKI AKAN MAGAGGANUN MANYAN MALAMAI TARE DA SAYYADI UMAR CHOBBE (kashi N’a 1)

    TA’ALIKI AKAN MAGAGGANUN MANYAN MALAMAI TARE DA SAYYADI UMAR CHOBBE (kashi N’a 1).

     

    MAULANA SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI Yana Cewa;

     

    “Mu Kiyayi Yima ANNABI (S.A.W) Shishshigi Akan Lamuran Addini Dan Yafi Kowa Sanin Ya Kamata, Dukkan Wata Da’awa Wacce Take Nuna Ba’a Yarda a Aurar Da Yarinya Ba Har Sai Ta Kai Shekara Sha Takwas (18) ‘Bata Ne, Idan Har Musulmi Ne Yake Wannan Da’awar Ya Tuba Ya Bari Idan Kuma Ba Musulmi Bane To Ya Kiyayi Bakin Shi Don Bashi Da Hurumin Shiga Maganar Addinin Da Ba Nashi Ba,

     

    Idan Ka Saki Zuciyarka Har Ta Ayyana Maka Aurar Da Yarinya ‘Yar Kasa Da Shekara Sha Takwas Zalunci Ne To Ka Sani Kamar Kana Tuhumar;

     

    Sayyadina Aliyu(R.A)

    Sayyadina Umar(R.A)

     

    Kai Har Ma Da ANNABIN Kan Shi Don Dukkansu Sun Aikata Wannan Abu,

     

    Me Kake Tunanin Abar Mace Da Namiji Balagaggu Waje ‘Daya Kuma Wai a Koya Musu ‘Sex Education’ (Ilmin Jima’i) To Ta Yaya Za’a Yi Gwajin??? Ashe Za’a Yi ‘Barna Kenan,

     

    Shekara Sittin Muka Yi Da Nasara (Turawa),Basu Rude Mu Ba, Sai Bakin Nasara Ne Zai Rude Mu, LA’ILAHA ILLALLAH….,

     

    KADA MU YARDA WANI YA SHIGO CIKINMU YA CI MUTUNCIN ANNABIMMU, KAWAI ANA SO A NUNA MA DUNIYA CEWA ANNABI (S.A.W) YA AIKATA KUSKURE(A’UZHU BILLAHI)”.

     

    ALLAH YA TSARE MANA IMANIN MU

  • DARUSA AIKIN HAJJ: Yanda Zaka Gudanar Da Aikin Hajji Cikin Sauki.

    ABUBUWAN DA AKE SO MAI SHIGA MAKKA YA YI…

     

    An so ga duk wanda zai shiga garin Makka ya yi wanka da niyyar shiga garin. Bayan wankan da mai Hajji ko Umura ya yi na ɗaura Harami, an so idan zai shiga Makka ya yi wani wankan, amma ba dole ba ne.

     

    An so ga wanda zai shiga Makka ya kwana a wurin da ake ce ma Ziɗuwan saboda Annabi (SAW) da ya zo, ya kwana a nan. Ana so mutum idan zai shiga garin, ya shiga ta saman Makka (da yake garin kamar tudu da kwari ne).

    Ana so idan mutum ya shiga Makka bayan ya ajiye kayansa a amintaccen masauki, ya yi gaggawan zuwa Harami. Ya shigo ta Babus Salam (a da; nan ne Babub Bani Shaiba take, sannan da ka shigo ga ƙofar Ka’aba nan). Idan za a shiga, a tabbatar da yin ƙanƙan da kai ga Allah kuma a karanta wannan addu’ar, “A’uzu billahil aziym, wa bi wajhihil kariym, wa sulɗanihil ƙadiym minas shaiɗanir rajiym bismillahir rahmanir rahim, bismillah, allahumma salli ala Muhammadin wa alihi wa sallim, allahumma agfirliy zunubi, waftahali abwaba rahmatika”.

     

    Ma’anar addu’ar ita ce, “Allah ina neman tsari da kai, ya Ubangiji maigirma, da hasken fuskarka (yadda ya dace da shi) maigirma, da sarautarka dauwamammiya, daga shaiɗani abin jefewa, da sunanka Allah, Allah ka yi salati ga Annabi Muhammad (SAW) da ‘ya’yan gidansa, ka yi aminci a gare shi. Allah ka gafarta mun zunubina, Allah ka buɗe mun ƙofofin rahamarka.”

     

    Ba a Harami ba kawai, a kowane Masallaci an so a karanta daga kan salatin Annabin nan zuwa ƙarshen addu’ar idan za a shiga.

    Idan mutum bai iya wannan addu’ar ba, ya yi a’uziyya da bisimillah da salatin Annabi (SAW) da kuma addu’ar da ya iya.

     

    Ana so da zarar mutum ya shiga idanunsa sun kalli ɗakin Ka’aba, ya ɗaga hannu ya nuna ɗakin ya ce “Allahumma zid haazhal baita tashriyfan wa ta’aziyman wa takriyman wa mahaabatan wa zid man sharrafahu wa karramahu min man hajjahu awi’itamarahu tashriyfan wa takriyman wa ta’aziyman wa birran, Allahumma antas salamu wa minkas salamu fahayyina rabbana bissalam.”

     

    Ma’anar addu’ar ita ce “Allah ka ƙara wa wannan ɗakin ɗaukaka da girma da kwarjini, Allah duk wanda ya girmama shi, ya daraja shi a tsakanin wanda ya hajja ce shi ko ya yi umura, shi ma ka ƙara ma sa ɗaukaka da girma da buwaya da tsoronka da bin ka. Allah kai ne aminci, daga wajenka aminci yake zuwa, mun gaida Ubangijinmu tare da sallama.”

     

    Daga nan sai mutum ya nufi Hajrul As’wad ya sumbance shi da bakinsa, idan bai samu iko ba ya shafa da hannu sai ya sumbanci hannun, idan ma wannan bai yiwu ba, to ko daga nesa yake ya nuna wurin dutsen da niyyar ya taɓa sai ya sumbance shi da hannu. Akwai alamar da aka sanya na tiles wanda aka ja layi da shi tun daga Hajral As’wad ɗin har zuwa bango har cikin gine-ginen saitin wurin, a nan mutum zai tsaya ya yi sumbar idan bai samu isa kaiwa ga dutsen ba. Daga nan sai ya fara ɗawafi.

     

    Hajral As’wad yana da girman daraja a Musulunci, Annabi (SAW) ya ce “duk wanda ya sumbance shi zai yi ma sa shaida a ranar Tashin ƙiyama.” Sannan ya zo a Hadisi cewa dutsen hannun daman Ubangiji ne (yadda ya dace da shi).” Ire-iren waɗannan Hadisin ba a iya gane haƙiƙanin ma’anarsu sai dai a karɓe su a matsayin ibada.

     

    Idan an shiga Ka’aba ba a yin nafilar gaisuwar Masallaci, ɗawafin da Alhaji ko mai Umura zai yi shi ne yake makwafin nafilar, amma ga wanda ba Hajji ko Umura yake yi ba, shi zai iya yin nafilar. Idan kuma mai yin Aikin Hajji ko Umura ya shigo ya ga an tada sallar farilla, sai ya bi, ba zai ce sai ya kammala ɗawafi ba. Koda mutum yana cikin ɗawafin ne aka tsaida sallar farilla, zai yanke ɗawafin ya tsaya daidai inda yake ya kabbara sallah. Ana yin sallama sai ya ci gaba da yin ɗawafin.

     

    Kamar yadda muka yi bayani a baya, ana fara ɗawafi ne daga Hajrul As’wad bayan an sumbance shi ko an shafe shi ko ɗaga hannu. Mutum zai sanya Ka’aba a hagunsa sai ya ce “Bismillah wallahu akbar, Allahumma imanan bika wa tasdiyƙan bikitabika wa wafaa’an bi ahdika wattiba’an lisunati Nabiyyika.”

     

    Ma’anar addu’ar ita ce “Ina farawa da sunan Allah, Allah kai ne maigirma, zan yi ɗawafin nan ne don imani da kai da gaskata littafinka da cika alƙawarinka da bin sunnar Annabinka (SAW)”.

     

    Haka mutum zai je ya kewayo, sai ya riƙa ƙirgawa duk lokacin da ya zo kan layin nan da ya fara ɗawafin daga kansa har ya yi guda bakwai. Idan namiji ne, ana so ya yi sassarfa a kewaye na ukun farko, sauran kuma ya yi tafiya Idan kuma an cika da yawa ta yadda mutum ba zai iya yin sassarfar ba sai ya yi tafiya kawai, babu komai. Amma mata ba su yin sassarfa, duka nasu tafiya ce.

     

    Ka’aba tana da kusurwowi guda biyu, Kusurwar Hajrul As’wad da ake farawa da ita, sai kuma wasu guda biyu da aka yi musu shinge su biyu ta yadda mutum ma ba zai iya taɓawa ba (Tarihi ya nuna cewa waɗannan kusurwowin biyu, nan ne lokacin da ƙuraishawa suke gina Ka’aba da kuɗinsu na halas ya ƙare sai suka datse ginin), su waɗannan ba a taɓa su ko an zo wucewa ta wurinsu. Amma idan mutum ya kewayo kafin ya zo Hajrul As’wad akwai Kusurwar Rukunil Yamani wanda shi ma ana shafarsa idan an samu hali, idan babu hali sai a nuna shi da hannun dama. Za a riƙa yin haka a duk kewayen ɗawafin da za a yi.

     

    Ana so a yawaita Zikirin Allah da addu’o’in da mutum ya zaɓa ya yi, don Malamai sun ce babu wata addu’a da aka ce dole ita za a yi. Sai dai wanda Hadisi ya kawo na Hajral As’wad. Addu’o’in da ake rubutawa a littafan nan da ake karantawa na Aikin Hajji masu kyau ne amma ba wai dole sai su ba. Idan mutum yana ɗawafi sai ya yawaita faɗin Subhanallah wal-hamdulillah wa la’ilaha illallah wallahu akbar wa laahaula wa laa ƙuwwata illa billahil aliyyil aziym, kamar yadda Ibn Majah ya ruwaito.

     

    A wurin Rukunil Yamani kuma, Abu Dawuda da Imamus Shafi’i sun ruwaito Hadisi daga Annabi (SAW) ya ce idan aka zo nan za a iya karanta “Rabbana atina fid dunya hasanatan wa fil-akhirati hasanatan wa ƙina azaban nar”. Akwai Mala’iku a wurin da za su amsa wa mutum da amin. Za a iya yin wannan addu’ar a lokacin gudanar da ɗawafin baki ɗaya.

     

    Zuwa mako mai zuwa za mu ci gaba da wani darasin cikin yardar Allah inda za mu kawo yadda Manzon Allah (SAW) ya yi aikin Hajji. Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadi wa ala alihi haƙƙa ƙadrihi wa miƙdarihil aziym.

  • WASU TAMBAYOYI DA AKA YIWA FARFESA IBRAHIM MAKARI (H) DA KUMA AMSOSHINSU

    WASU TAMBAYOYI DA AKA YIWA PROFESSOR IBRAHIM MAKARI (H) DA KUMA AMSOSHINSU

     

    …..Yaa Sheikh mene ban-banci tsakanin NAFSU da RUHU da QALBU?

     

    Akwai_littafi_da Imamu Ghazali ya wallafa akan wadannan, amma dai dukansu sukanzo da maana kusan daya, idan an nufi janibin shaawa da soye soyen rai sai a ce mata Nafsu, idan an nufi janibin sabanin gangan jiki sai a ce Ruuh, idan an nufi qudurce qudurce sai a ce Qalb. Wannan amsar ba zata gamsar daga komawa zuwa ga littafai ba.

     

    Mai bada amsar ma ya taba yin Majlisi akan raino da yaye a hanyar Allah, yayi magana mai dan tsawo akan wadannan. (A iya neman Cassette)

     

    Don Allah Malam, ina neman ingancin wannan Hadisin:

    في حكمة مجامعة النساء وهي

    وصية النبي صلى الله عليه وسلم لعلي بن أبي طالب رضي الله عنه قال النبي :

    :

    Acikin hikmar Saduwa Da Maata, Kuma wannan wasiyya Ce Da Daga Manzon Allah saw Zuwaga Sayyidna Aliyu bn Abi Dalib rta.

    :

    يا علي لا تجامع المرأة في نظر النجوم فإذا كان فيه الولد يكون كاذبا.

    :

    Ya Aliyu kada ka sadu da iyalinka acikin KALLON taurari (wato a sararin samaniya) Idan Aka Samu ciki a wannan Saduwa to zai kasance maqaryaci.

    :

    ولا تجامع المرأة في حيضها فإذا كان فيه الولد يكون أبرص وأجذم.

    :

    Kada ka sadu da MACE a lokacin haila, idan Allah swt Ya Hukunta samun ‘Da to zai kasance da cutar kuturta.

    :

    ولا تجامع المرأة والناس يسمعون صوتها فإذا كان فيه الولد يكون سفيها.

    :

    Kada ka sadu da MACE alhalin mutane suna Jin sautin ta, idan Allah swt Ya Hukunta samun ‘Da to zai kasance Wawa ko gaula ko ga’bo.

    :

    ولا تجامع المرأة وقت الضحي والنهار فإذا كان فيه الولد يكون مجنونا.

    :

    Kada ka sadu da MACE a lokacin hantsi ko kuma da Rana tsaka, idan Allah swt Ya hukunta samun ‘Da to zai kasance Mahaukaci.

    :

    ولا تجامع المرأة وهي تنطر النجوم فيكون الولد عاصيا لله ورسوله.

    :

    Kada ka sadu da MACE alhalin tana KALLON taurari a sama, idan Allah ya hukunta samun ‘Da to zai kasance mai Sabon Allah da Manzon SA.

    :

    ولا تجامع المرأة وهي كارهة فيكون الولد عاقا لوالديه.

    :

    Kada ka sadu da MACE Akan tilas, idan Allah ya hukunta ‘Da to zai kasance mai rashin biyayya Ga mahaifansa uwa da UBA.

    :

    ولا تجامع المرأة وأنت تنطر فرجها فيكون الولد أعمي.

    :

    Kada ka sadu da MACE kana mai KALLON farjinta, idan Allah ya hukunta ‘Da to zai kasance Makaho.

    :

    ولا تجامع المرأة ليلة الأضحي ويومها فيكون الولد سفاك الدماء.

    :

    Kada ka sadu da MACE daren Babbar sallah da kuma ranar ta, idan Allah ya Hukunta ‘Da to zai zamo Dan Ta’ adda mai zubar da jini.

    :

    ولا تجامع المرأة آخر الأربعاء من الشهر فيكون الولد عدوَّ الله و النبي والمسلمين

    :

    Kada ka sadu da MACE a larabar karshen ko wane wata na Musulunci, idan Allah ya Hukunta ‘Da to zai zamo maqiyin Allah da Manzon Allah da kuma Musulmi baki daya.

    :

    AMSA: Wannan hadisin Kagagge ne!

     

    Shehi, ina aikin bautar kasa NYSC a kudu, makarantar da nake koyarwa suna da tsarin gabatar da addu’a ranar Juma’a da Litinin, dukansu Kiristocine ni kadaine Musulmi. Ya halatta na rinka shiga anayin addu’o’in nasu dani?

     

    Bai halatta ka shiga cikin Adduan da ka tabbata za a yi Shirka da Allah cikinsa ba, amma idan ana gudun wata fitina a Addinin Mutum babu laifi ya shiga a Zahiri amma a Zuciyarsa yana qudurta qin hada Allah da waninsa.

     

    Ya ingancin hadisin da ake cewa Maaiki SAW yace Wanda yayi bushara da zuwan Ramadan wuta ba zata ci shi ba? Shin ya halatta afadi labarin zuwansa?

     

    Kuskure ne danganta wa Manzon Allah (SallallLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) wannan maganar; domin bai fada ba…

     

    Sannan ana tabbatar da tsayuwar watan Ramadhan ne a ranar 29 ga watan Sha’aban kaman yanda shari’ar Musulunci ta tanadar.. Zai yiwu a ga wata a ranar, zai kuma yiwu wata ya ki bayyana ta yanda sai an cika kwanaki 30..

     

    Saboda haka a guji yada wannan sanarwa mai cike da kuskure.. Akwai kuskuren danganta wa Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) abin da bai fada ba, ga kuma kuskuren lissafin wata na al-qamariyya..

     

    Allah shi ne masani na hakika.

     

    Shin yaya niyyar azumin nafila take, shin idan mutum baiyi niyyar azumin ba har alfijiri ya keto, shin zai iya cigaba da azuminsa?

     

    Babu wata ibada da take inganta ba tare da niyya ba, ita kuma niyya wurin ta na asali shi ne zuciya.

     

    Hadisi ya inganta daga Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) yana cewa: ((Duk wanda bai kwana da niyya ba ba shi da Azumi..)) ; saboda wannan magana ta Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) ya sa malamai suka tafi akan rashin ingancin Azumi na farilla da ba a daura masa niyya ba..

     

    Akwai kuma wani Hadisin da yake nuna cewa Sayyiduna Rasulullah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) a wata rana ya wayi gari babu abin karyawa a gidansa, sai kuwa ya ce ai sai mu cigaba da Azumi, ma’ana dai sai bayan alfijir ya dauki niyyar yin Azumin, amma dai wannan a Azumin nafila ne, saboda haka malamai suka ce zai yiwu a yi Azumi na nafila ba tare da an kwana da niyya ba..

     

    Amma dai dole shi ma a dauri niyyar a lokacin da aka yi shirin dauka, ma’ana mutum ya kudurce a zuciya cewa zai yi ibadar Azumi ta nafila.. Allah ya karbi ibadun mu

     

    Inaso Prof. Yadanyi tsokaci akan mas’alar gaisawa da mace (wadda ba muharramarka ba).

     

    Haramun ne a mazhabar Malikiyya da Shafi’iyya mudlakan, sawa’un macen tsohuwa ce ko budurwa, a mazhabar Hanafiyya da Hanbaliyya kuma haramun ne idan macen budurwa ce, amma ya halatta idan tsohuwa ce wadda ba a shalawarta..

     

    Allah shi ne masani na hakika. Ameeeen

  • Shin Akwai Aljanu Yan Darikar Tijjaniyya Kamar Yanda Sheikh Dahiru Bauchi RA Yake Fada. ???

    SHIN AKWAI ALJANU YAN ĎARIQAR TIJJANIYYA KAMAR YADDA AKE YAĎAWA MAULANMU SHEHU ĎAHIRU BAUCI YA FAĎA?

     

    Banji hakikar abinda Maulanmu Shehu Ďahiru Bauci ya faďa kan wannan qadhiyya ba, sai dai koma yaya lamarin ya kasance wannan magana bata saba da shari’a ba balle ta zamto abin yin Isgili ga wannan babban bawan Allah da ya karar da rayuwar sa cikin hidimar Musulunci.

     

    Tamkar yadda mutane suke firaq daban daban Ahlussunah,Shi’a mu’utazila da Yan Izala haka abin yake cikin Aljanu.

     

    Allah ya faďa mana cikin qur’anin sa mai girma game da firaq na Aljanu.

     

    وَأَنَّا مِنَّا الصَّالِحُونَ وَمِنَّا دُون ذَلِكَ كُنَّا طَرَائِق قِدَدًا

    ( Daga cikin mu akwai Salihai akwai waďand basu ba, mun kasance tafarkai ne mabanbanta)

     

    Al’imamu Alqurďubi ya hakaito daga Suddiy yana lokacin da yake fassara طرأئق قددا.

     

    Yace 👉 السدي في قوله تعالى { طرائق قددا} قال : في الجن مثلكم قدرية، ومرجئة، وخوارج، ورافضة، وشيعة، وسنية. وقال قوم :

     

    Alhafiz Ibn Katheer cikin tafsirin sa karkashin wannan aya ya kawo kissar Sulaiman bin Mihrãn Al’a’amash yadda yayi magana da Aljani har ya tambaye shi abincin da yake so ya kawo mashi sannan ya tambaye shi Su Waye Rãwafidh cikin ku (Aljanu) sai Aljanin yace sune mafiya sharrin mu.

     

    سمعت الأعمش يقول تروح إلينا جني فقلت له ما أحب الطعام إليكم فقال الأرز قال فأتيناهم به فجعلت أرى اللقم ترفع ولا أرى أحدا فقلت فيكم من هذه الأهواء التي فينا قال نعم فقلت فما الرافضة فيكم قال شرنا

     

    Ibn Katheer yace ” Na karantawa Shehina Mizzi isnãdin wannan kissa yace min ta inganta”

     

    Kenan a wajen Malamai ba sabuwar magana bace ace an sami Aljani ďan ďariqa ko wata firqa.Wanda dama mu yan Tijjaniya bamu shakka ko kaďan akwai Aljanu masu tarin yawa da suke Tijjaniya.

     

    Haka kuma akwai Aljanun da suke bin tafarkin Bidi’a na Wahabiyya wanda waďannan Aljanu masu shiga jikin Yan mata su hana su Aure saboda…

     

    Allah ya kara wa Shehi lafiya. Amiiiin

Back to top button