ƘALUBALEN DA SUFANCI KAN IYA FUSKANTA NAN GABA.
A bisa al’ada, sufaye ko sufanci ba su da ƙalubalen da ya wuce MUNKIRAI da MUNKIRANCIN SU.
Shi munkiri shine Wanda bashi da ilimin sufanci, baya kan tafarkin su, ko kuma yana dauke da kiyayyar su a zuciyar sa, kuma yake ƙin yarda ko isgili ko shishigi akan abinda ya shafi Sufanci alhalin bashi da hasken imanin da zai fahimce ta.
Amma nan gaba, matsalar da sufanci za ta iya fuskanta ba daga wurin maqiyya ko munkirai bane, daga wurin masu da’awar sufanci ne wayanda ba su da ma’arifa a kirjin su, sai a kwakwalwar su (ilimin littafi).
Wasu daga cikin wayanda ake yiwa kallon jagorori a sufanci a yau, suna kokarin daura matasa akan ilimin littafi a cikin lamarin sufanci, ba tare da kokarin daura su akan tafarkin yawaita zikiri fiye da haddace littafin ba, hakan kuma kuskure ne domin Shehu Gibrima yana cewa “MAN LA WIRDA LAHU, LA WARIDA LAHU” wato Duk wanda baya wuridi/azkar (na taraqqi), babu waridi (kwaranyar ilimi daga Allah direct) gare sa.
Da wannan waridin ne sufaye suka bambanta da sauran al’ummar Annabi, domin suna kara samun haske daga Allah akan abinda kai dasu kuka sani wanda kai baka samu.
To ire-iren wayannan matasa, sune zasu dinga hawa mumbari nan gaba suna da’awar su sufaye ne, suna ƙaryata AHWAL saboda karantawa suka yi amma basu ɗanɗana ba, ballantana su gaskata abinda ma’abota AHWAL din suka ji ko suka gani ko suka faɗa. Sai dai kaji suna cewa “Ba haka sufi wane ko Shehu wane yace abu kaza yake ko akeyi ba”, amma su a gashin kansu, ba zasu iya bayanin “experience” din su akan abun ba.
Da wannan nake so in ja hankalin matasa irina, Ilimi shine jagorar dukkan ayyuka tabbas, amma idan bai samu muhalli a zuciya ba, muddin a kwakwalwa ya tsaya, toh duk abinda hankali bai fahimta ba, ma’abocin ilimin nan ba zai aminta da wannan abun ba. Shi kuma Sufanci gaba dayansa, aikin IMANI ne ba Hankali ba.
Sannan masu bada ijaza, su ji tsoron Allah su duba cancanta kamar yadda aka duba cancantar su aka basu ba tareda sun tambaya ba. Kuma Kai da aka ba ijazar, kaji tsoron Allah ka nemi cikakkiyar sani akan aiki da ita, ka jarraba komai akan ka, kasan ta ka fahimce ta kafin ka daura ya’yan jama’a.
Allah ka cigaba da tsarkake mana Tijjaniyyar mu, ba domin mu ba, don hidimar Shehu Abulfathi da aminan sa a gidan Shehu Atiku RTA.
✍️Sidi Sadauki