INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN
Marubuci Kuma Mahaddacin Kur’ani, Muhammadu Dan Katambawa Ya Rasu
Daga Mukhtar Lawan Liver Gwarzo
Anyi babban rashin Gangaran ka fi Gwani mahaddaci kuma marubucin Littafin Allah Alqur’ani a fadin karamar hukumar Gwarzo dake jihar kano.
Alaramma Malam Muhammadu Dan Katambawa ya rasu ne a jiya Talata, kuma an yi jana’izar sa kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Allah Ya jikanshi da rahama ya gafarta masa Albarkacin Annabi ﷺ da Alkur’ani Amin.