Tunatarwa

  • AKWAI DARASI MAI TARIN YAWA WAJEN KYAUTATA ZATO GA ALLAH SWT.

    A KARANTA DA KYAU DOMIN AKWAI DARASI MAI TARIN YAWA WAJEN KYAUTATA ZATO GA ALLAH UBANGIJIN RAHMA:

     

    Wata mata ta je gurin Annabi Dauda (AS) cikin fushi, ta ce masa: “Ya Annabi Allah! Ubangijinka yana da adalci kuwa?

     

    Sai ya ce: “Kwarai kuwa, mai adalci ne, ba ya zalunci.

     

    Menene labarin ki?

     

    Sai ta ce: “Ni bazawara ce, ba ni da mai taimaka min, ga ‘ya’ya mata guda 3 marayu. Ina ciyar da su ne da sana’anar saka da nake yi.

     

    Jiya na yi sakata mai yawa, na daure a wani jan tsumma, zan tafi kasuwa na sayar, na sami abin da zanciyar da kaina da ‘ya’yana, sai wani tsuntsu ya zo ya wafce daga hannuna. Kuma ba ni da komai, ga marayu.

     

    Kafin Annabi Dauda (AS) ya ce komai ga wannan mata, sai ga wasu mutane su 10 sun shigo, kowannen su da Dinare 100 a hannunsa, suka ce:

     

    “Ya Annabi Allah! Muna son za mu yi sadaka da wannan kudi..

     

    Sai Annabi Dauda (AS) ya ce da su: “Me ya faru?” Sai suka ce: “Muna cikin jirgin ruwa, sai iska mai karfi ta taso, jirgin namu ya bule, sai muka dinga ambaton Allah, kuma muka yi bakancen idan Allah Ya tseratar da mu, za mu yi sadaka da Dinare dari-dari.

     

    Muna cikin wannan hali, sai wani tsuntsu ya jeho mana wani jan tsumma, a cikin tsumman akwai wata saka.

     

    Sai muka toshe bular da wannan sakar, Allah Ya tseratar da mu.

     

    Sai Annabi Dauda (AS) ya yi godiya ga Allah, ya fuskanci wannan mata ya ce mata: “Ubangijinki mai adalci ne.

     

    Idan kin yi sakar nawa kike siyarwa?”

     

    Sai ta ce: “Dirhami daya”.

     

    Sai ya ce: “Ga Dinare 1000, Allah Ya sayi sakarki, karbi ki je ki ciyar da ‘ya’yanki”.

     

    Allahu Akbar

     

    Allah yasa mudace duniya da lahira Bijahi Rasulillahi (S.A.W). Amiiiin Yaa ALLAH

  • FALALAR GANIMA GA AL’UMMAR ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) A WATAN AL~MUHARRAM.

    FALALAR GANIMA GA AL’UMMAR ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) A WATAN AL~MUHARRAM.

     

    ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) YA FADA YACE: “DUK WANDA YAYI AZUMI A JUMA’A TA FARKON WATAN

     

    ﺍﻟﻤﺤﺮ ﻡ

     

    ALLAH ZAI GAFARTA MASA ZUNUBAN SA WANDA YA WUCE NA SHEKARUN BAYA”.

     

    2. ANNABI (Sallallahu Alaihi Wasallam) YACE: “DUK WANDA YAYI AZUMIN KWANAKI UKU A CIKIN WATAN

     

    ﺍﻟﻤﺤﺮ ﻡ ﺍﻟﺨﻤﻴﺲ = ﻭﺍﻟﺠﻤﻌﺔ = ﻭﺍﻟﺴﺒﺖ =

     

    ALLAH ZAI SA A RUBUTA MAKA/SA LADAN IBADAR SHEKARA DARI BAKWAI (700)”.

     

    3. WANDA YAYI AZUMIN KWANAKI KOMA (10) NA FARKON WATAN “ﺍﻟﻤﺤﺮ ﻡ” ALLAH ZAI BAKA/SA ALJANNA FIRDAUSI MADAU KAKIYA”.

     

    ALLAH KABA MU FALALAR WATAN DA SIRRIN WATAN DAN ALFARMAN ANNABI MUHAMMADU (Sallallahu Alaihi Wasallam). Amiin Yaa ALLAH

  • ASRARUN DA AKEYI NA KARSHEN SHEKARA DAGA HALARAN MAULANMU SHEIK USMAN KUSFA ZARIA.

    FA’I’DAN SABON SHEKARA

     

    Muna Farin Cikin Zuwan Sabon Shekara Na Addinin Musulunci (Islamic Calendar).

     

    ASRARUN DA AKEYI NA KARSHEN SHEKARA DAGA HALARAN MAULANMU SHEIK USMAN KUSFA ZARIA

     

    Wanda Yayi Wannan Sirrin Daren Karshe Na Watan Zulhijja Ko Kuma Ranar Farko Na Watan Almuharram,.

     

    ANNABI SAW Yace: Duk Wanda Yayi Allah Zai Mashi Gafaran Dukkan Zunuban Dake tsakaninsa da Allah Ta’alah sannan Kuma Allah Zai Karbi Dukkan Ibadunsa kuma Sheidan Zaije Yana Ihu Yana Kuka Yana Cewa: “YA KAICONSHI YA HASARANSHI YA TABEWANSHI, YA WAHALA TSAWON SHEKARA YANA SANYAKA ZUNUBAI AMMA GASHI KA BATA AIKINSHI A RANA DAYA”

     

    GA YADDA SIRRIN YAKE:

     

    • Mutum Zaiyi Nafila Raka’a Goma (10) a cikin Ko Wace Raka’a Zai karanta Fatiha kafa Daya Ayatul Kursiyyu Goma (10) Qulhuwallahu (10) Goma.

     

    Idan Ya Idar Sai Ya Daga Hannayensa Ya Karanta Wannan Adduan:

     

    “RABBI IGFIRLY , WALIWALIDIYYA WALI JAMI’IL MUMININA WAL MUMINATI AL AHYA’I MINHUM WAL AMWATI ” kafa Goma (10).

     

    Sannan Kuma Ya kara da Wannan Adduan:

     

    “ ALLAHUMMA MA AMILTU FI HAZIHISSANATI MIMMA NAHAITANY ANHU FALAM ATUB MINHU WALAM TARDHAHU WA NASITUHU WALAM TANSAHU WA HALIMTA ALAYYA BA’ABDA QUDRATIKA ALA UQUBATY WA DA’AUTANY ILA TTAUBATI BA’ADA JARA’ATY ALA MA’ASIYATIKA FA INNY ASTAGFIRUKA FAGFIRLY YA GAFURU, WAMA AMILTU FEEHA MIN AMALIN MIMMA TARDHAHU WA WA’ADTANY ALAIHI SSAWABA, FA AS’ ALUKALLAHUMMA YA KAREEMU YA ZALJALALI WAL IKRAM AN TATAQABBALHU MINNY WALA TAQDA’A RAJA’I MINKA YA KAREEMU WASALLAHU ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN WA ALA ALIHI WA SAHBIHI WASALLIM”

     

    —- Kafa Uku (3).

     

    Allah ya bamu duk Alkhairan dake shekaran Kuma Yasa Shekaran Farincikinmu ne Albarkacin Annabi Muhammadu SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM. Amiin Yaa ALLAH

Back to top button