Al’amarin Ba Haka Yake Ba, Akan Na MANZON ALLAH(S.A.W), JININSA Da BAWALINSA Ba Najasa Bane, Sam.

JINI Ko BAWALI/FITSARI;

 

A Bisa Hankali Da Al’adar Zamantakewa JINI Ko FITSARI/BAWALI Najasa Ne(Musamman a Duniyar Musulmai An Tabbatar Da Cewa; JINI Ko FITSARI/BAWALI Najasa Ne Kai Tsaye),

 

Kuma Ta Fuskar Malaman Lafiya(Likitoci) Guba Ne, Na Kowa Haka Yake,

 

To Amma Al’amarin Ba Haka Yake Ba, Akan Na MANZON ALLAH(S.A.W), JININSA Da BAWALINSA Ba Najasa Bane, Sam.

 

Saboda Me???

 

Saboda Suna Da Dangane/Alaƙa Ta Kai Tsaye Da MANZON ALLAH(S.A.W), Hasalima An Sha Su, An Samu Lafiya, An Warke Sumul,

 

Karatun Da Nake So Na Fitar Anan Shi Ne; Duk Abin Da Yake Da Dangane/Alaƙa Da MANZON ALLAH(S.A.W), To Yafi Ƙarfin Kushe Ko Muzantawa Komai Ƙanƙantarsa Kuwa, Don Haka Ne;

 

👉 IYAYEN MANZON ALLAH(S.A.W),

👉 IYALAN MANZON ALLAH(S.A.W),

👉 MATAN MANZON ALLAH(S.A.W),

👉 SAHABBAN MANZON ALLAH(S.A.W),

👉 KAYAN MANZON ALLAH(S.A.W),

👉 DABBOBIN MANZON ALLAH(S.A.W),

👉 GARIN MANZON ALLAH(S.A.W),

 

Da Sauransu,

 

Duk Sun Fi Ƙarfin a Taɓa Su, Ko a Muzanta Su Saboda Suna Da Nasaba Ta Kai Tsaye Da MANZON ALLAH(S.A.W).

 

Don Haka Masu Taɓa Mutumcin IYAYEN ANNABI(S.A.W) Sai Ku Shafawa Kanku Ruwa, Ku Kiyaye.

 

Kun Ji Dai FITSARI/BAWALI Ko JININ MANZON ALLAH(S.A.W) Ma Yafi Ƙarfin Muzantawa Balantana IYAYEN ANNABI (S.A.W).

 

Ga Abin Da QADHI IYAD(R.A) Ya Ce a Hakkin MANZON ALLAH(S.A.W);

 

“KO FITSARIN DABBAR DA ANNABI (S.A.W) YAKE HAWA, IDAN MUTUM YA CE FITSARINTA WARI YAKE, TO HUKUNCINSA KIIISAA NE!”

 

– (QADHI-IYAD MAI ASHIFAH SHI YA RUWAITO HAKAN).

 

ALLAH KA ƘARA TSARE MANA IMANIN MU DAGA RUƊANIN ZAMANI, YA ƘARA MANA ƘAUNAR SAYYIDUL-WUJUDI (S.A.W) AMEEEN

Share

Back to top button