An Gudanar Da Gagarumin Zikirin Juma’a Da Yiwa Kasa Addu’a A Garin Ibadan Jihar Oyo.

Zikirin Jumma’a Tare Da Yiwa Kasa Addu’a Daga Ibadan

 

A Yammacin Ranar Juma’a Ne 25/12/202, Aka Gudanar Da Gagarumin Wazifa Da Zikirin Jumma’a Da Yiwa Kasar Mu Nigeria Addu’an Wanda Ya Gudana A Garin Ibadan Jihar Oyo.

 

Taron Wanda Aka Gudanar Dashi Karkashin Jagoranci Gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR Wanda Khadimul Faidah Alhaji Ibrahim Sheikh Tahir Usman Bauchi R T A Ya Jagoranta A Babban Masallacin Garin Ibadan.

 

Taron Ya Samu Hallatar Manya Baki Daban Daban Daga South West Gabadaya Shehanai Mukaddamai Da Muridai Tare Da Khalifan Darikar Tijjaniyya Na Jihar Lagos Sheikh Tijjani Imam Da Kuma Sheikh Khalifa Ibrahim Inuwa (Sabo Ibadan) Khalifan Darikar Tijjaniyya Na Jihar Oyo.

 

Muna Addu’an Allah Ya Kara Wa Maulana Sheikh Dahiru Bauchi RA Lafiya Da Nisan Kwana.

 

Maulana Khalefah Ibrahim Inuwa Allah Ya Ingata Lafiya Ya Kara Ja Mana Kwana Ya Karbi Addu’o’in Mu Ya Namu Zaman Lafiya A Kasashen Duniya Baki Daya. Amiin

Share

Back to top button