An Yi Wa Sheikh Usman Zariya Kyautar Ɓalli Ta Tabarmar Sheikh Ahmadu Tijjani (RTA).

An Yi Wa Sheikh Usman Zariya Kyautar Ɓalli Ta Tabarmar Sheikh Ahmadu Tijjani (RTA).

 

Murna ya ɓarke a Zawiyyar Sheik Usman Idris dake bKusfa Zariya tun bayan da Shehin ya fito da wani ɓalli ta tabarmar da Sheikh Ahmadu Tijjani (RTA) yake gudanar da halwa bisa ita a lokacin da yake raye, almajiran shehin da daman gaske sun shaida da haka a wannan Zawiyyar.”

 

Ya Bayyana haka ne in da ya ci gaba da cewa; wani lokaci ne da Sheikh Ibrahim Inyass (RTA) ya kai ziyara zuwa ƙasar Maroko aka bashi kyautar tabarmar shi ma daga nan ya samo ta shi aka ɓallan ma shi domin samun tabarrakin Sheikh Ahmadu Tijjani (RTA).

 

Sheikh Usman Kusfa Zaria yana bayyana kamomin waliyai musamman Almajiran Sheikh Ahmad Tijjani RA wanda haka ya jawo cece kuce a kafar sada zumunta na Facebook.

 

Allah ya saka masa da Alkhairi ya karawa Maulana Sheikh lafiya. Amiin

Share

Back to top button