Gwamnan Bauchi Ya Dauki Nauyin Karatun Mahaddatan Alqur’ani Guda Uku Zuwa Kasar Indiya
ABIN A YABA: Gwamna Bala Ya Dauki Nauyin Karatun Mahaddatan Kur’ani Guda Uku Zuwa Kasar Indiya
Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya sha alwashin gwamnatinsa za ta cigaba da tallafawa matasa maza da mata daga kowane bangare domin ganin sun cimma kudirorinsu na rayuwa.
Gwamnan ya fadi hakan ne a yayin da ya karbi bakoncin Ibrahim Mohammed Nasir, wanda ya samu kambun Gwarzon Shekara na gasar karatun kur’ani ta duniya da aka gudanar a kasar Saudiyya.
Gwamna ya kuma taya Hafizan su uku bisa yadda suka karawa jihar Bauchi martaba da kima a idon duniya, inda ya yi musu alwashin zai cigaba da tallafa musu.
Gwamnan ya kuma roke su da su kasance wakilai nagari ga jihar Bauchi fa Nijeriya ta hanyar mayar da hankali wajen karatunsu.
Hafiz Nasir da sauran takwarorinsa guda biyu, an dauki nauyin karatun na su ne ta hannun kwamishinan ma’aikatar harkokin addini, Yakubu Ibrahim Hamza.
Daga Lawal Muazu Bauchi
Babban mai taimakawa Gwamna Bala
Kan harkokin sabbin kafafun sadarwa