Hukuncin Wasa Da Wazifa A Cikin Darikar Tijjaniyya.
HUKUNCIN WASA DA WAZIFA
A littafin fiqhun dariqa mai suna SU’AL WA JAWAB, Shehin yace abubuwa uku ne sharadin shiga da fita daga Tijjaniya kamar haka:
1. Ba a yarda ka ziyarci wani waliyyi rayayye ko matacce ba wanda ba dan Tijjaniya bane da niyyar neman albarkar sa, amma zaka iya ziyartan Annabawa da Sahabbai ka nemi albarkar su.
2. In aka karba, ba a cewa za a daina har abada ballantana a daina lazumi ko wazifa ko Zikirin Juma’a.
3. Ba a yarda ka hada dariqar Tijjaniya da wata dariqar ba na sauran waliyai.
Sai mutum ya aminta da haka za a bashi dariqa. Idan kuwa ya saba daya daga ciki, ya yanke ratayuwa da yayi da shehu Tijjani, shi ba batijjane bane. Sai har in ya koma anyi masa tajdidi (an sake bashi dariqar) wurin muqaddami.
Da gangan saboda dukiya ko wani abu na son zuciya ba rashin lafiya ba, ba yaqi ba, ba mantuwa ba, zakaga samarin mu da yanmatan mu suna qin yin wazifa. Sai sun ga baqon shehi sai suce ayi musu tajdidi, gobe ma su sake shagala.
Toh shehin ya cigaba da cewa “wanda ya dauki Tijjaniya wasa, yau yayi, gobe ya qiyi, jibi yace ayi masa tajdidi, ana ji masa tsoron zaiyi mummunar mutuwa” Allah ya tsare mu!
Shiyasa duk abinda muka sa a gaba yake yi mana wuya saboda mun fifita son duniya akan Annabi SAW. Wannan dariqar fa direct in muqaddami zai baka, babu shi sai Annabi SAW, amma a haka kake iya watsi dashi, in ance ina masoya Annabi SAW kaje GAKU NAN.
Yan’uwa, mu sani duk abinda yake ba Allah ba, watarana zai gushe. Kar mu yarda halitta ta raba mu da mahaliccin mu. Rashin yin wazifa a jam’i ga maza da gangan, karya alqawari ne. Karya alqawari kuwa munafurci ne, munafurci kuwa yafi kafurci.
Kowa yaje ya samu muqaddami yayi masa tajdidi, a koma a riqe zawiya da kyau!
Daga: Sir Sadauki