MAGAGGANU MALAMAI AKAN AZUMIN ASHURA TARIHIN FARA SHI, YADDA AKE YINSHI DA FALALARSHI
AZUMIN ASHURA TARIHIN FARA SHI, YADDA AKE YINSHI DA FALALARSHI
A Musulunci akwai watanni 12, Hudu daga ciki Masu Alfarma ne, kamar yadda yazo a Tauba aya 36, to Almuharram na cikinsu Wadanda aka yi Umurni a Yawaita Azumi a cikinsu
Kari akan haka, Kuma Annabi ya sake yin Umurnin Yawaita Azumin cikinsa har yace: Ba Wani wata da Allah yafi so a Yawaita Azumin cikinshi bayan Ramadan kamar Almuharram
ASALIN FARA AZUMIN ASHURA, A MAKKA
Bukhari/Muslim daga Aishat RA, tace Quraishu ta kasance tana Azumin Ashura, lokacin Jahiliyya Kuma Annabi saww ya kasance Yana Azuminsa, Kuma yayi horo ayi …..
CIGABA DA ASHURA A MADINA
Bukhari/Muslim daga Ibn Abbas RA, Lokacin da Annabi saww ya zo Madina, sai ya samu Yahudawa na Azumin Ashura, yace, Meye haka? Suka ce, Rana ce ta Kwarai, da Allah ya tserar da Musa AS, da Bani Isra’il daga Makiyin su, sai Annabi saww yace: Nafi Ku cancanta da Musa, sai yayi Azumin yayi horo ayi
MATSAYIN AZUMIN ASHURA
Bukhari/Muslim daga Mu’awiya dan Abu Sufyan RA, yace: Naji Annabi saww yace: Yau ne Ranar Ashura Amma ba a wajabta maku Azumin ta ba, Amma ni zan yi Azumin, Wanda yaso yayi Azumi Wanda yaso yaci Abinci.
HADA SHURA DA TASU’A
Bukhari/Muslim Abu Musal Ash Ariy RA Ranar Ashura ta kasance Yahudawa na girmamata suna Rikon ta Ranar IDI, sai Annabi saww yace Amma Ku dai (Kawai) kuyi Azuminta
Bukhari/Muslim daga Ibn Abbas RA, da Annabi saww yayi Azumin Ashura yayi horo ayi Azumin sai suka ce: Ya Manzon Allah, Rana ce da Yahudawa da Nasara ke girmamawa sai yace: idan badi tazo a Riwayar Muslim idan nakai badi insha Allah, zan yi Azumin 9_10 wato TASU’A da ASHURA ( Sai Bai Kai ba saww)
YADDA AKEYI AZUMIN ASHURAR
Malamai sunyi bayanin hanyoyi 3, da akeyin Azumin:
1_ Ayi Azumin 9, 10 da 11, don ka samu Ladar Azumin Watan baki dayanshi
2_Ayi 9 da 10 (Tasu’a da Ashura) kenan Koko 10-11
3 _Ko a kalla ayi Ranar Ashura 10 ga watan kenan, shine Mafi Karanci
LADAR AZUMIN ASHURA
Muslim daga Abi Qatadat RA, yace An tambayi Annabi saww, kan Azumin Ashura sai yace: “Yana Kankare Zunubin Shekarar da ta Gabata”
Yaku Masu Imani kar mu Manta Allah na kar6a Addu’ar Mai Azumi, Musamman lokacin Buda Baki, mu roki wa Kasa da Jahohinmu zama lfy.
Abdulhakeem Ahmad Ya’akub Gusau 05/08/22
07/Almuharram/1444@H