Musulmai kimanin miliyan biyu daga faɗin duniya sun taru a Dutsen Arafat.
Musulmai kimanin miliyan biyu daga faɗin duniya sun taru a Dutsen Arafat da ke kudu maso gabashin birnin Makkah inda za su wuni suna gudanar da ibada, kamar yadda yake a rukunan Aikin Hajji.
Ana yin Tsayuwar Arafat ranar 9 ga watan Dhul-Hijja, inda maniyyata suke gudanar da addu’o’i daban-daban.
Ana gudanar da Aikin Hajjin bana ne a yanayi na tsananin zafi, ko da yake hukumomin Saudiyya sun ɗauki matakai don rage zafin da ake fama da shi.
Allah ya karbi ayyukan mu da Addu’o’in mu baki daya albarkan Annabi ﷺ. Amiin