SAYYIDA AMINA(R.A) Ɗiyar Wahab Ɗan Abdi-Manafin, Mafificiyar Mace Ce a Cikin Ƙuraishawa, Wajen Ƙwakwalwa Da Kuma Kyawawan Ɗabi’u.

ITA CE; MAHAIFIYAR RAHMAR DUNIYA DA LAHIRA(S.A.W);

 

SAYYIDA AMINA(R.A) Ɗiyar Wahab Ɗan Abdi-Manafin, Mafificiyar Mace Ce a Cikin Ƙuraishawa, Domin Ta Banbanta Da Sauran Mata a Wajen Ƙwakwalwa Da Kuma Kyawawan Ɗabi’u.

 

Tana Daga Cikin Mazauna Makkah, Kuma An Ce: Yanayin Harshenta Yana Nuni Da Cewa Ita ‘Yar “Yathrib” Ce, Mahaifinta Wahab Ya Rasu Ya Barta, Inda Amminsa Wahaib Ya Ci Gaba Da Rainon Ta.

 

Abdul-Muɗallib Ya Nemawa SAYYIDUNA ABDULLAHI(R.A) Ɗansa Auren SAYYIDA AMINA(R.A), Kuma ALLAH(S.W.T) Ya Albarkaci Aurensu Da Haifar SAYYIDUNA MUHAMMADU(S.A.W), SAYYIDUNA ABDULLAHI(R.A) Yayi Tafiya Domin Kasuwanci Zuwa Birnin Gaza(Kasar Palasdinu),

 

SAYYIDA AMINA(R.A) Ta Haifi SAYYIDUNA RASULULLAHI(S.A.W) Lokacin Da Ya Iso Yathrib(Madina) a Hanyar Shi Ta Komawa Gida Makkah, Sai Rashin Lafiya Ta Kama SAYYIDUNA ABDULLAHI(R.A), Kuma Ya Rasu Anan.

 

SAYYIDA AMINA(R.A) Ta Kasance Tana Tafiya Duk Shekara Daga Makkah Zuwa Yathrib Domin Ziyartar Kabarin Mijinta SAYYIDUNA ABDULLAHI(R.A) Da Kuma Dangin Mahaifinsa Bani-Adiyyin Bin Annajjar Sannan Ta Koma Gida.

 

SAYYIDA AMINA(R.A) Ta Yi Rashin Lafiya Akan Hanyarta Ta Komawa Gida(Daga Madinah) Kuma ALLAH Yayi Mata Cikawa a Wani Guri Da Ake Ƙira ‘AL ABWA’ Tsakanin MAKKAH Da MADINAH.

 

Ta Bar Ɗanta SAYYIDUNA RASULULLAHI(S.A.W) Maraya Ba Uwa Ba Uba. Shekarun Shi Shida a Wannan Lokaci.

 

Ya ALLAH! Ka Yi Mana Luɗufi a Cikin Dukkanin Al’amuranmu Don Alfarmar SAYYIDA AMINA(R.A) Mai Girman Daraja, Kuma Mahaifiyar MasoyinKa SAYYIDUNA RASULULLAHI(S.A.W) Ameeeen

Back to top button