Takaitaccen Tarihin Sheikh Ahmad Tijjani RA Shugaban Waliyai Kashi Na Goma Sha Biyar 15.

CIKAMAKIN WALIYAI (15)

 

HIJIRAR SA ZUWA FAS

 

Kamar yadda Annabi SAW yayi hijira daga makka zuwa Madina bisa dalilin tsana da tsangwamar makiyya Allah, haka Shehu Tijjani bisa dole yayi hijira daga Abu Samguna zuwa Fas saboda mulkin kama karya da turkuwa suke yi a wancan lokacin. A ranar 17 ga watan Rabi’ul Auwal 1213H Shehu Tijjani tareda iyalin sa da Almajirin sa Sidi Aliyu Harazumi da Sidi Muhammadul Mishiri RTA, sun isa garin Fas a ranar 6 ga watan Rabi’us sani 1213H, a lokacin shekarun Shehu Tijjani 63. A ranar sai Shehu Tijjani ya daure dabbobin sa a masallacin Jami’ar Ƙarawin, jama’a suka yi korafi kan cewa ai zasu lalata wurin da fitsari da kashi, Shehu Tijjani yace ba zasu yi ba, haka kuwa ya faru, washegari jama’a suka yi mamakin wannan karamar na Shehu Tijjani RTA.

 

A gidan iyayen Sidi Aliyu Harazumi aka sauke Shehu Tijjani da iyalan sa, nan da nan labarin sa ya cika Fas saboda ilimi, hikima da karamar sa, sarkin Fas Maulaya Sulaiman, ya samu labarin Shehu Tijjani har yaso ya kulla alaƙa dashi amma malamai masu hassada da Shehu Tijjani suna kushe shi, har saida Alƙali Sidi Abdulƙadir ya wanke Shehu Tijjani a wurin Maulaya Sulaiman, Sannan ya gayyace shi cikin da’irar malaman ƙasar. Watarana wani gwani yana tafsirin Suratun Nas, Maulaya Sulaiman yace wa Shehu Tijjani ya tofa albarkacin bakinsa kan abinda gwanin ya faɗa, Shehu Tijjani yayi masa gyara da sharhi wanda duk malaman saida suka yi mamakin ilimin Shehu Tijjani, shi kuma Maulaya Sulaiman nan ya yarda lallai Shehu Tijjani yana saduwa da Annabi ido da ido kamar yadda ake fadi a gari, don haka shima sai ya nemi Shehu Tijjani ya sada shi da Annabi SAW, Amma ko sadu da Annabi ido da ido, bai iya jure hasken ba dole ya suma, bayan ya farka ya sallamawa Shehu Tijjani ya karɓi Ɗariƙar sa nan take sannan daga baya ya ba Shehu Tijjani gida a inda ake kira “Darul Miraya” ya zauna kyauta amma Shehu Tijjani kowani wata sai ya bada kudin hayan gidan ga mabuƙata bisa iznin Annabi SAW saboda tsammanin gidan na masarauta ne ba na Maulaya Sulaiman ba.

 

Wata biyu bayan zaman sa a Fas ya umurci Sidi Aliyu Harazumi ya rubuta littafin “Jawahirul Ma’ani wa bulugul Amani fiy faidhi Abul Abbas Tijjani”, littafin da ya ƙunshi muhimman ilimomin Shari’a da Sufanci baki ɗaya.

 

ZAWIYYAR FAS

 

A farko, Shehu Tijjani da Almajiran sa suna wazifa ne a farfajiyar gidan sa, wani lokaci a zawiyoyi daban-daban, sai Annabi SAW ya umarce shi da ya gina nasa zawiyyar, Shehu Tijjani ya nemi kufai a “Dardas”, Duk da dai kufan yana da ban tsoro, babu mai iya shiga shi kaɗai, har ma wani majazubi mai suna Sidi Lahabi yakan kara kunnen sa a kofar kufen yana jiyo muryoyi kamar ana zikiri.

 

An fara ginin zawiyar ne 4 ga watan Rabi’ul Auwal 1214. Maulaya Sulaiman ya aiko kuɗi mai yawa domin gina masallacin, Amma Shehu Tijjani yaƙi karɓa, yace “Wannan ginin yana hannun Allah ne kai tsaye”.

 

Kafin a fara ginin, Shehu Tijjani ya rubuta wani Ismul A’azam a bisa babban dutse sannan a gana ya rubuta “Ya ubangiji na saboda sunan ka mai girma, ka kare almajirai na daga ƙaf zuwa ƙaf”, wato daga bangon duniya zuwa daya bangon, sannan yasa aka binne dutsen a inda aka tayar da ɗaya daga cikin dirkokin masallacin, wanda ake kira “Dirkar Zinari”.

 

Bayan kammala ginin, majazubin nan wato Sidi Lahabi yace “Fas ta sake zama rayayya, musamman ma dai Dardas”.

 

Mafi yawan lokuta in Shehu Tijjani yana zaune da sahabbansa a zawiyyar, sai ya tashi ya leƙa waje yana kallon dama da hauni yana murmushi, da suka tambaye shi dalili sai yace “Ina duba zawiyyar ne yadda take yanzu ne da yadda zata koma nan gaba wurin faɗi da tsawo”, gashi kuwa yanzu yadda ya misalta girman, haka ya kasance.

 

ABUL ABBASI MAULANA WALIYULLAHI TIJJANI.

 

✍️ Sidi Sadauki

Share

Back to top button