TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA GOMA SHA TARA (19)
TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 19.
HIJIRAN ANNABI (SAW) DAGA MAKKA ZUWA MADINA (Fitan Annabi (SAW) daga garin Makka)
Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain
Annabi Muhammad (SAW) tareda Sayyidina Abubakar sun fita daga Makka a Wannan darenda Quraishawa sukayi niyyan kashe Annabi Muhammad (SAW), tare dasu da Amiru Ɗan Fuhairata, da Ɗan jagoransu kuma Abdullahi Ɗan Uraiqidil-Laisi.
Sun tafi cikin wannan dare zuwa Kogon ‘Thaur’, sun bawa Ɗan jagoransu abun hawansu yatafi dasu, amma yadawo musu dasu bayan kwana 3.
Yayinda Quraishawa suka wayi gari suka tabbatar da Sayyidina Ali shine a kan gadon Annabi Muhammad (SAW), kuma Annabi Muhammad (SAW) ya fita a Makka zai tafi Madina, sai suka saka Taguwa (Mecen Rakumi) 100 kyauta ga duk Wanda ya kawo Annabi Muhammad (SAW) a Raye ko a mace. Haka suka Gama nemansu Basu ga Annabi Muhammad (SAW) da Sahibinsa Sayyidina Abubakar ba Tsawon wannan kwanakin.
Bayan sunyi kwana 3 a cikin Kogon ‘Thaur’, sai Dan jagoransu ya dawo, yazo musu a ababen hawansu kaman Yadda suka fada masa, suka dauki hanya domin cigaba da Hijirarsu zuwa Madina.
Tsayawa da sukayi kwana uku a Kogon’Thaur’ sunyi ne domin su ɓatar da kafa, Quraishawa suyi tunanin sun isa Madina, su daina nemansu. Bayannan sukuma sai su fito su tafi a tsanake.
Allah ya kara haskaka zukatanmu da kaunar Annabi Muhammad (SAW), ya kara mana himma wajen koyi dashi a fili da ɓoye. Amin.
07032509197
yaseen9253@gmail.com