Tarihin Rayuwar Sheikh Ahmadu Tijjani RA (Cikamakin Waliyai) Kashi Na Hudu 4.

CIKAMAKIN WALIYAI (4)

 

IYAYE DA YAN’UWANSA (RTA)

 

Mahaifin Shehu Ahmad Tijjani wato Sayyidi Muhammad (RTA) ya kasance babban malami masanin Alqur’ani da Sunna kuma mai matukar kiyaye umurni da hanin Allah, mai kokarin kiran halittun Allah zuwa ga tafarkin shiriya, ya rayu bisa cin halal tsantsa, yawan zikiri da ibadu daban-daban, ya samu yardar Allah (wulaya) har ma rauhanai sukan ziyarce shi da kyautar dukiya da abubuwa daban-daban amma sai ya ce su tafi, shi baya bukatar komai daga wurin halitta sai dai daga wurin mahalicci.

 

Mahaifiyar Shehu Ahmad Tijjani kuwa wato Sayyida Aisha (RTA), mace ce mai tsarkin nasaba kamar yadda muka kawo a baya, ta samu cikakken tarbiyya da ilimin addini daga iyayen ta, kuma sai Allah ya aura mata waliyyi a matsayin miji, shiyasa ta rayu ita ma bisa abinda mijin nata yake kai na ibada cike da tsoron Allah.

 

Ta haifi yara da yawa suna mutuwa a ƙananan shekaru amma bata yi baƙin cikin haka ba domin ta yarda Allah ke bayarwa kuma ya karɓa a lokacin da yaso domin ya jarrabi imanin bayin sa. Daga karshe Allah sai ya raya mata yar ta mace mai suna Rukayya, sannan ta haifi Shehu Ahmad Tijjani, kana daga bisani tayi masa ƙani mai suna Muhammad wanda ake yi masa laƙabi da Ibn Umar.

 

Allah ya kara musu yarda, Amin!

 

✍️ Sidi Sadauki

Back to top button