MANZON ALLAH (S.A.W) Ya Hau a Daren ISRA’I DA MI’IRAJI, Ta Kasance a Cikin ‘Yan Uwanta Burakoki.

BURAQAH:

 

Wacce MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Hau a Daren ISRA’I DA MI’IRAJI, Ta Kasance a Cikin ‘Yan Uwanta Burakoki, Amma Ta Rame Bata Ci Bata Sha Saboda Tsananin Bege Da Tunanin ANNABI(S.A.W).

 

Shi Yasa Mala’ika Jibreel(A.S) Ya Zabo Ta Ya Taho Da Ita Domin Taga MASOYINTA(S.A.W).

 

Kuma Kafin Ya Hau Bayanta Sai Da Ta Nemi Wasu Alfarmomi Guda Biyu a WajenSA(S.A.W).

 

TA CE:”Ya Jibreelu Ka Gaya Ma Wannan Masoyi, Ma’abocin Fuska Mai Kyau Da ‘Kyalkyali, INA SO YA SANYA NI A CIKIN CETONSA.. KUMA INA SO YA LAMUNCE MIN IN ZAMA ABIN HAWANSA A FILIN AL-QIYAMAH”.

 

Nan Take MANZON NA MU(S.A.W) Ya Ce;”NA LAMUNCE MIKI”.

 

YA ALLAH Ka Azurta Mu Da Tarayya Da Shi Zahiran Wa Batinan.. Fid-Dunya Wal-Akhirah.

 

“Sallu Alaihi Wa Sallimu Tasleeman”.

Share

Back to top button