TARIHIN SAYYADA FATIMAH YAR’ MANZON ALLAH (SAW) Kashi Na Biyu (2).

JIMADA THANI Watan Haihuwar Tsokar Jikin MA’AIKI(S.A.W); NANA FATIMA AZ-ZAHRA’U

 

3⃣ LADUBBANTA/SUNAYENTA;

 

Daga Cikin Ladubbanta Akwai;

 

Ma’asuma,

Mazluma,

Karima,

Sabira

Mabaruka,

Da Sauransu.

 

Ya Zo a Hadisi Cewa; ‘NANA FATIMA(A.S)’ Tana Da Sunaye Guda Tara a Wajen ALLAH Maɗaukakin Sarki;

 

1. FAƊIMA: Ma’anar Faɗima Ya Zo Da Ma’anoni Daban-Daban a Ruwayoyi, Amma Ma’anar Da Tafi Shahara Ita Ce; ALLAH Ta’ala Ya ‘Yanta Ta Daga Wuta Da Dukkan Masu Sonta.

 

2. SIDDIƘA: Ma’ana Mai Yawan Gaskiya Ko Mai Gaskiya a Dukkan Zantukanta Ko Kuma a Wata Ma’ana Mai Yawan Gasgatawa Ga Saƙon Da Mahaifinta Ya Zo Da Shi.

 

3. MUBARAKA: Ma’ana Ma’abociyar Albarka.

 

4. ƊAHIRA: Ma’ana Tsarkakakkiya Daga Dukkan Najasa Ta Zahiri Da Baɗini.

 

5. ZAKIYYA: Ma’ana Tsarkakakkiya Daga Dukkan Munanan Ɗabi’u.

 

6. RABIYYA: Ma’ana Yardarta Da Hukunci Ko ‘Kaddara Ta ALLAH Ta’ala.

 

7. MARDIYYA: Ma’ana Yardajjiya a Wajen ALLAH Maɗaukakin Sarki.

 

8. BATULA: Ma’ana Wadda Ba Ta Jinin Al’ada Na Mata Kamar Jinin Haila Ko Na Nifasi-Biƙi.

 

9. ZAHRA: Ma’ana Wadda Take Da Haske Na Zahiri Da Baɗini, a Wata Ruwaya Ya Zo Akan Cewa; Ana Ce Ma Ta Zahra Ne Saboda Idan Tana Ibada To Haskenta Yana Bayyana Ga Ma’abota Sama Wato Mala’iku Kamar Yadda Hasken Taurari Yake Bayyana Ga Ma’abota ‘Kasa(Wato Mutane).

 

4⃣ KINAYARTA;

 

Haƙiƙa Tana Da Kinaya Masu Yawa Amma Waɗanda Suka Fi Shahara Sune;

 

*. Ummul-A’immah

*. Da Kuma Ummu Abiha.

 

Daga: Imam Anas

 

ALLAH Ka Sanya Mu Cikin Jerin MASOYA NANA FATIMA(A.S), Ya Ƙara Mana ƘaunarTA(A.S).

 

  • Amincin ALLAH Ya Ƙara Tabbata Ga CIKAMAKIN ANNABAWA DA MANZANNI (S.A.W). AMIIN YAA ALAH

Share

Back to top button