KA SANI YA KAI MURIDI…
Ɗariƙarmu ta Tijjaniyya, babu wanda yake da ikon cewa mallakinsa ce kuma babu mai iya barazanar korar kawai saboda wani saɓani ya haɗa ku. Shehin kowa a cikin wannan ɗariƙa Maulanmu Shehu Tijjani, ne Maulanmu Shehu Ibrahim Niasee, kuma shi ne babban Halifa a cikinta.
Kabar tsayawa kula da masu danganta kansu da mallakar wannan ɗariƙa, suna ganin su ne kaɗai masu sanyawa ko hanawa. Sannan kar sake ka tsaya duban masu kaddamar Shehunan su a matsayin masu sanyawa ko kuma hanawa a kan abin da kwata kwata babu shi a cikin fikihun ɗariƙar ko dan suna ganin irin gudunmawar da suke bayarwa ga ɗariƙar Eh, gudunmawar da suke bayarwa na iya sanya su zama jiga-jigan wannan ɗariƙar amman ba masu sanyawa da hanawa ba.
A tarihi babu wani malami da ya bayar da gagarumar gudunmawa ga wannan ɗariƙar da ma addinin musulunci kamar Maulana Shehu Ibrahim Niasse, duk da haka bai taba da’awar mallakar wannan ɗariƙar ba balle har ya kira kansa a matsayin Shehin da ya ke sanyawa ko kuma hanawa a karan kansa sai dai kawai yana yin nuni ne da abin da fikihun wannan ɗariƙar ya tanadar.
Sheikh Abdulbaƙi Miftah, a cikin littafinsa mai suna واء على الشيخ أحمد التجاني وأتباعه”, ” a babi na biyar wanda ya ƙunshi bayanin irin yanda almajiran Shehu Tijjani, da kuma magadansa su kai ƙoƙari wajen yaɗa wannan ɗariƙar tamu.
Marubucin ya yi ƙoƙarin fitar da kididigar mutanen da suka karbi ɗariƙar Tijjaniyya, daga hannun manyan manyan Halifofin Shehu Tijjaniyya ya kuma bayyana cewa Shehu Ibrahim Niase shi ne ya fi kowa girma, a yaɗa ɗariƙar domin ta hanyarsa sama da mutane miliyan 30 ne suka karɓi ɗariƙar kai tsaye.
Duk da irin wadannan nasarori, da Shehu ya samu amman a lokuta da dama yana cewa Shehunai na guda biyu ne akwai na zahiri da kuma na ɓoye Shehunan zahiri su ne Alkur’ani da kuma Sunnar shugaba Sallallahu alaihi Wa sallama, wanda kuma mun san babu wanda ya fi Shehu fahimtar su Shehinsa kuma na ɓoye yana cewa shi ne Maulana Shehu Tijjani, wanda yake tare da shi a ko da yaushe.
Shi sanya ma da Sheikh Ahmad Sukairij da ya zo yabon Shehun ya ke cewa cewa…
وإني أرى الشيخ التجاني خـاتـمـا
وأنت الذي قد صرت في الخاتم الفصا
Ka sani ya kai ɗan’uwana muridi ɗariƙar ba ta kowa ba ce wanda idan ya kore ka shi kenan ka koru ɗariƙar ta Shehu Tijjani ce duk wani Shehi wakili ne idan ka ga Shehin da kake tare da shi ya gaza ta fuskar sauke nauyin wakilci saboda
Dalili wanda ya bayyana kana damar canja shi kuma babu abin da zai faru da kai domin ba bautarwa ba ce bawa da mai shi kowa daga kogi Shehu Tijjani yake sha.