RASUWA

  • Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un: Allah ya yiwa Sheikh Ahmad Ba rasuwa dake Dakar a kasar Senegal.

    Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un

     

    Munyi babban rashi a Khaulaha dake Senegal.

     

    Allah ya yiwa Sheikh Ahmad Ba rasuwa dake Dakar a kasar Senegal.

     

    Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa. Amiin

     

    Tijjaniyya Media News

  • Allah Ya Yiwa Sheikh Ibrahim Inyass Rasuwa a Kasar Murtania.

    Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un 😭😭

     

    ……Allah ya yiwa jikan Sheikh Ibrahim Inyass rasuwa a kasar Murtania.

     

    Allah ya karbi rayuwar Alhaji Abdullahi dan Sheikh Alhaji Almushri kuma jikan Sheikh Ibrahim Niasse RTA ta wajen Sayyida Rabi’atu Niasse rasuwa.

     

    Allah ya jikanbsa ya sada shi da kakan sa Annabi Salallahu Alaihi wa Alihi Wa Sallam. Amiin

     

    Daga: Aliyu Uthman Bashir

  • Allah ya yiwa daya daga cikin manyan Shehunan Tijjaniyya a Nijar Khalifa Sheikh Ibrahim Shu’aihu Niamey rasuwa

    INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN

     

    Allah ya yiwa daya daga cikin manyan Shehunan Tijjaniyya a Nijar Khalifa Sheikh Ibrahim Sheikh Shu’aihu Niamey rasuwa.

     

    Khalifa Sheikh Shu’aihu babban malamin Musulunci ne kuma shehin Ɗarikar Tijjaniyya a Africa, yana zaune a birnin Niamey dake kasar Niger.

     

    Kafin rasuwan sa yayi rubuce-rubuce da dama a bangaren addini ya kuma bada gudumawa sosai don tabbatar da darikar Tijjaniyya a Niger

     

    Ya rasu yana da shekara 61 a duniya.

     

    Allah ya jikan Sheikh Shu’aihu da rahma ya gafarta masa, ya jaddada rahma a gare shi Albarkacin Annabi ﷺ. Amiin Yaa ALLAH.

     

    Daga: Babangida A Maina

    Tijjaniyya Media News

  • Innalillahi Wa’inna Ilahir Raji’un Sheikh Abdulbaki El-Hüseyni Ya Rasu A Kasar Turkiya

    Innalillahi Wa’inna Ilahir Raji’un

     

    Babban malamin Islama kuma dan Tijjaniyya Shaykh Abdulbaki El-Hüseyni ya rasu a Turkey.

     

    Sheikh Abdulbaki El-Huseyni ya bada gudumawa akan yada addinin Musulunci shine wanda yake bude wuraren taimakawa al’ummar don kare su daga hanyoyin shaye-shaye da kuma miyagun kwayoyi.

     

    Shaykh Abdulbaki El-Hüseyni shine shugaban kungiyar Jama’ah mafi girma a Turkiyya kuma jagora a bangaren addini.

     

    Ya rasu bayan yayi fama da rashin lafiya, anyi masa Jana’iza kamar yadda Addini ya tanadar. Allah ya kwautata namu.

     

    Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa, ya yafe masa kura – kuran sa. Amiiiin Yaa Allah

  • Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un: Jikar Shehu Ibrahim Nyass, Wato Sayyada Hafsatu Usman Bashir Ta Rasu.

    INNNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN

     

    Jikar Shehu Ibrahim Nyass, Wato Sayyada Hafsatu Usman Bashir Ta Rasu

     

    Marigayiyar ɗiya ce ga Sayyada Ummuhani Sheikh Ibrahim, Muna mika sakon ta’aziyya ga daukacin yan’uwa masoya musamman Sayyada ummahani tare da yan uwanta.

     

    A madadin Ofishin gudanarwa na kamfanin jaridar Tijjaniyya Media News karkashin jagoranci Babangida Alhaji Maina muna mika sakon ta’azziya ga yan’uwa Masoya da iyalan Alhul Inyass Allah ya jikan ta da rahma ya gafarta mata.

     

    Allah ya jikan ta da rahma ya gafarta mata. Amiiiin

     

    Daga: Tijjaniyya Media News

Back to top button