RASUWA

  • Babban Limamin Oyo, Sheikh Mashood Abdul Ganiyy Adebayo Ajokidero III Ya Rasu.

    Babban Limamin Oyo, Sheikh Mashood Abdul Ganiyy Adebayo Ajokidero III ya rasu.

     

    Daga: Babangida A. Maina

     

    Shahararren malamin Musulunci kuma shehin darikar Tijjaniyya a kudancin najeriya Sheikh Mashood Abdul Ganiy Adebayo Ajokidero III ya rasu a birnin Ibadan jihar Oyo.

     

    Jaridar Tijjaniyya Media News ta ruwaito cewa ya rasu ne da sanyin safiyar yau alhamis 26/01/2023, Sheikh Mashood Abdul Ganiy Adebayo Ajokidero shahararren malamin tsangaya addinin islama ne a fadin najeriya wanda ya bada gagarumar gudumawa wurin daukaka Addinin Musulunci a kudancin najeriya.

     

    Muna addu’an Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa, Allah ya karbi shahadar sa. Amiin

     

    Daga; Babangida A. Maina

    Tijjaniyya Media News

  • Matashin Malamin Dan Tijjaniyya Ya Rasu Amb Gwani Sukairiju A Garin Kano.

    Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un 😭😭

     

    …..Mahaddata Alkur’ani Sunyi Babban Rashi.

     

    Allah Ya Yiwa Amb Gwani Sukairiju Kila Rasuwa Yanzu Mutumin Kirki Wanda Ya Sadaukar Da Rayuwarsa Wurin Yiwa Addinin Allah Hidima.

     

    Za’ayi Gudanar Da Sallar Jana’izarsa Yau Asabar 21/01/2022/3, Da Karfe 2:00 Na Rana A Maƙabartar Hajj Camp Dake Birnin Kano.

     

    Allah Ka Jaddada Masa Rahma, Ya Jikan Gwani Da Rahma, Allah Ka Karɓi Hidimar Da Ya Yiwa Addinin Musulunci Da Alkur’ani Mai Girma.

     

    Muna Addu’an Allah Ya Jikan Iyayen Mu, Da Malaman Mu Baki Daya, ALLAH Yasa Mu Cika Da Imani. Amiiiin

     

    Daga: Shafin Faidah

  • Allah Ya Karbi Rayuwar Sheikh Goni Modu Goni Zahrami RTA Dake Birnin Maiduguri, Borno.

    الموت لايضرمن سعدا بل هوراحةلمن قدرشدا

    Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un 😭😭

     

    Allah Ya Karbi Rayuwar Sheikh Goni Modu Goni Zahrami RTA Dake Birnin Maiduguri, Borno.

     

    Sheikh Goni Modu Goni Zahrami Babban Malamin Islama A Najeriya Kuma Masanin Alkur’ani Mai Girma.

     

    Kafin Rasuwan Sa Yana Kaeantar Da Ashifi Inda Duban Jama’a Suke Halartan Karatun Sa Daga Sassa Daban Daban Na Fadin Najeriya Dama Makwafta.

     

    Hakika Munyi Babban Rashin Masoyi Mai Hidima Ga Addinin Musulunci Dama Alkur’ani Mai Girma.

     

    Muna Rokon Allah (swt) Ya Sadashi Da Annabin Rahama (SAW) Ya Jaddada Rahma A Gare Shi. Amiin Yaa ALLAH

     

    Babangida A Maina

    Tijjaniyya Media News

  • Inna’lillah: Gobara Taci Magidanci Tare Da Iyalan Sa A Zaria.

    INNA’LILLAH WA’INNA ILAIHI RAJI’UN

     

    Gobara Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Miji Da Matarsa Da Ya’yansu Biyu A Daren Jiya Alhamis.

     

    Matar mai suna Bilkisu M Sani da mijinta da ya’yansu su biyu, sun mutu ne a gobarar da ta tashi cikin daren jiya a garin Zaria dake jihar Kaduna.

     

    Muna addu’an Allah ya jikan ta da rahma ya gafarta mata, tare da sauran yan’uwa Musulmai baki daya. Amiin

     

    Babangida A. Maina

    Tijjaniyya Media News

  • INNALILLAHI: Allah Yayiwa Sheikh Abubakar Wanda Akafi Sani Da (Malam Sidi) Bolari Rasuwa A Safiyar Yau Litinin.

    INNA’LILLAHI WA’INNA ILAIHIR RA’JIUN😭

     

    Allah Yayiwa Sheikh Abubakar Wanda Akafi Sani Da (Malam Sidi) Bolari Rasuwa A Safiyar Yau Litinin 2-01-2023.

     

    Za’ayi Jana’izar Sa Ayau Insha Allahu A Ƙofar Gidansa Dake Bolari Wajen Masallachin Filin Ƙwallo, Arewa Da Layin Babban Dam Na Ruwa, Da Misalin Ƙarfe 02:30pm.

     

    Shehu Malam Siddi Fitachchen Malami Ne Mai Matuƙar Tsantsaini Ga Tsoron Allah Ga Kuma Yawan Sallah Da Salatin Annabi Muhammadu S.a.w.

     

    Baya Ga Haka Ya Kasanche Yana Bada Karatun Ilimin Addini A Lokuta Mabambanta A Chikin Yini Guda, Inda Dayawa Daga Chikin Manyan Malamai Da Sauran Bayin Allah Su Kanje Garesa Domin Ɗaukar Karatun Na Fannoni Da Dama.

     

    Malam Siddi Chikakken Batijjane Ne Masoyin Manzon Allah S.a.w. Wanda Yanada Masallachi Inda Ake Karanta Wazifa, Sannan A Kowachche Shekara Akan Gabatar Da Maulidi A Ƙofar Gidansa Dake Nan Bolari.

     

    Marigayin Yabi Bayan Iyalinsa/Matar Sa Wadda Itama Allah Yayiwa Rasuwa A Makon- Nan Daya Gabata.

     

    Marigayiyar Tabar (Matar Sa) Ta Rasu Ta’ Bar Ya’ya’ Huɗu (4) Da Jikoki Talatin Da Sama (30+)

     

    Allah Yamusu Rahma Baki Ɗaya 🤲

     

    Muhammad Izzuddin Abubakarkar

Back to top button