DA GASKE NE KARANTA SALATIL FATIHI YAFI SAUƘAN ALƘUR’ANI DUBU SHIDA LADA ? 

DA GASKE NE KARANTA SALATIL FATIHI YAFI SAUƘAN ALƘUR’ANI DUBU SHIDA LADA?

 

Tambayar da ake min a kwanakin nan kenan, yin shiru ko kuma kau da kai daga wautar jahilai ba zai zamo mafita a garemu ba. Ga yadda abun yake.

 

Da farko mu fara sanin cewa lallai ko mun yarda ko bamu yarda ba salatil fatihi salatin Annabi sallallahu alaihi wasallam ne ingantacce, domin babu ambaton wani shehi ko wata Ɗariƙa a ciki sai sunan Allah da Annabi sallallahu alaihi wasallam da kuma ahlinsa masu daraja.

 

Akwai abun da ake cewa falala da daraja, zan bada misali domin sauƙin fahimtar menene falala da daraja.

 

Kaine aka baka dala 100 ta amurka da kuma Alƙur’ani izu sitti aka ce ka zaɓi ɗaya a ciki, ina da tabbacin mafi yawan mutane dalar nan zasu ɗauka su ƙyale Alƙur’anin, saboda meye? Saboda da wannan dalar zaka iya fansar Alƙur’ani sama da 50. Idan kuma Alƙur’anin ka ɗauka da iya shi kaɗai zaka tsira. A nan ba wai an ɗaukaka dalar akan Alƙur’ani bane a ah sai dan dalar tafi Alƙur’anin falala, shi kuma Alƙur’ani babu wani littafi da ya kaishi daraja da ɗaukaka a wajen duk wani musulmin kirki.

 

Wannan kenan, sannan a duk lokacin da ka karanta duk wani harafi na Alƙur’ani akwai adadin ladan da Allah yace zai baka, amma salatin Annabi sallallahu alaihi wasallam Allah ne da kansa yace zai maka salati shima. Ya girman ladan salatin da Allah zai yiwa bawansa yake? Bamu sani ba.

 

Saboda haka muke ƙara nanatawa lallai yiwa Annabi sallallahu alaihi wasallam salati aiki ne da babu wanda ya isa ya faɗa maka menene sakamakonka sai Allah.

 

Allah ya bamu dacewa Duniya da Lahira ya kuma ƙara mana ƙaunar Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wasallam. Amin

 

Mustapha Abubakar Kwaro

12/09/2023

Back to top button