DARASI MAI TAKEN: MUƘAMIN WALIYAI KASHI NA BIYU (2)
MUƘAMIN WALIYAI (2)
1. GAUSI: Shi ake kira Ƙuɗubul Gausi ko Ƙuɗubul Aƙɗab ko Insanul Kamil ko Al-Muktar ko Fardul Jãmi’i ko kuma Abdullahi.
Kalmar ƙuɗubi (قطب) na nufin “pole” a turanci, a hausa yana nufin tsani, ginshiƙi ko dirka. Wanda ya samu muƙamin wulaya har ya kai yana wakiltar wani sashi na gari ko na al’umma, ya zama ƙuɗubin wannan garin ko wannan al’ummar, alfarmar shi Allah zai dinga saukarwa wa’yannan jama’ar ruwan sama (arziki) ya kuma rangwanta musu yayin da suka cancanci a halakar dasu ko a saukar musu da mummunar bala’i. Shugaban ƙuɗuban nan gaba daya shine Gausu, wato (الغوث) a larabci, kuma yana nufin “mai taimako”, wato mai taimakon Halitta baki ɗaya.
Gausi shine khalifan Annabi ﷺ mafi girma kuma shine shugaban waliyai baki ɗaya, ba su iya tasrifi sai da sanin sa, shi kaɗai ne a zamanin sa har sai in ya rasu sannan a samu wani ya hau muƙamin sa. Shine Insanul Kãmil (cikakken mutum) saboda office din sa ne matattar cika (hadratul kamali), duk mutumin da ya samu wulaya ya shiga wannan office din, ya zama cikakken mutum, shine wanda Annabi ﷺ yake cewa ” Allah ba zai tashi kiyama ba muddin akwai cikakken mutum a doron kasa”.
2. IMÃMÃNI: Sune mafi kusanci da Gausi kuma su biyu ne, tamkar wazirai suke gareshi. Sune masu muƙamin “Mafatihil Kunuz” wato Muƙamin Siddiƙiyyah. Dayan su sunan sa Abdur-rabbi, ɗayan su sunan sa Abdul Malik. Ɗaya cikin su yana iyakar Alamil Malakuti, Ɗayan su yana iyakar Alamil Mulki, ɗayan su ne yake hawa muƙamin Gausi da zarar Gausin ya rasu.
3. AUTÃDU: Su huɗu ne, kowannen su yana kusurwa daya daga kusurwar duniya guda hudu, sune wayanda Allah ke cewa “wal jibalu Autada”, dasu Allah yake kiyaye kusurwar duniya, dayan su yana bisa muƙamin Sayyidina Abubakar a daman duniya, ɗaya yana muƙamin Sayyidina Umar a Haunin Duniya, ɗaya yana gabashin duniya a muƙamin Sayyidina Usman, ɗaya yana yammacin duniya a muƙamin Sayyidina Aliyu (Allah ya kara musu yarda).
Alhamdulillah, Allah Ya Bada Lada. Amiin
✍️ Sidi Sadauki