Gayyatan Mauludin Sheikh Ahmadu Tijjani RA Karo Na Tara (9) A Birnin Kebbi

ZA’A GUDANAR DA GAGARUMIN TARON MAULUDIN SHEIKH AHMADU TIJJANI RA A KEBBI

 

Gidauniyar Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR tana gayyatan daukacin al’ummar Musulmai zuwa gagarumin taron tunawa da Maulana Sheikh Ahmad Tijjani RA karo na tara (9), wanda zai gudana a birnin Kebbi dake jihar Kebbi.

 

Taron wanda ya kunshi makon Shehu, Zikirin juma’a da gabatar da wasu muhimman ziyarori da babban taron a filin wasa na garin Kebbi.

 

Za’a gudanar da taron kamar haka:

 

Rana: 01/September/2024

 

Lokaci: Karfe goma na safe 10:00am

 

Wuri: Filin wasa na Haliru Audu dake birnin Kebbi dake jihar Kebbi.

 

Akwai Manyan Baki Daga Sassan Fadin Duniya Da Zasu Halarta.

 

Allah yasa ayi lafiya a tashi lafiya. Amiin

Share

Back to top button