Sheikh Tijjani Shahararren Malamin Ne Wanda Ya Rayu Cikin Hidimtawa Addinin Musulunci.

SHEIKH TIJJANI USMAN ZANGON BARE-BARI

 

Wannan Shine Sheikh Tijjani Usman Zangon Bare-bari Dake Birnin Kano, Shahararren Malamin Ne Wanda Ya Rayu Cikin Hidimtawa Addinin Musulunci Da Darikar Tijjaniyya Wanda Ya Bada Gagarumin Gudumuwa Wurin Yada Darikar Tijjaniyya A Yammacin Africa.

 

Sheikh Tijjani Usman Babban Masanin Ne A Bangarorin Kamar Haka, Masanin Ilmin Alkur’ani Mai Girma, Da Tafsir, Fiqhu, Lugga, Nahwu Da Sauran Su. An Haifi Shehin Malamin A Shekara Ta 1914 Yayi Wafati A Shekara 1970 Yayi Shekaru 56 A Duniya.

 

Allah Ya Jaddada Masa Rahma Ya Gafarta Masa Allah Ya Kara Masa Kusanci Da Fiyayye Halitta Annabi Muhammadu ﷺ. Amiin

 

 

Babangida A. Maina

Share

Back to top button