SHEKARU 99 MASU ALBARKA: Sheikh Dahiru Bauchi RA Ya Cika Shekaru 99 A Lissafin Hijriyya.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi Ya Cika Shekaru 98 Duniya A Lissafin Hijriyya (1,346-1,444).
Shahararren malamin addinin Islama a fadin duniya kuma mataimakin shugaban masu fatwa na najeriya kuma babban shehin Darikar Tijjaniyya a duniya. Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA ya cika shekaru 98 a duniya a lissafin hijriyya (1,346-1444).
Sheikh Dahiru Bauchi an haife shi a karamar hukumar Nafada dake jihar Gombe, ya taso a gaban mahaifansa inda ya fara karatun Alkur’ani mai girma a gaban su, daga baya ya shiga neman karatun inda har Allah ya azurta shi da samun Alkur’ani mai girma tare da sauran littafan addinin Musulunci har ya zama masu shahara a wannan zamani.
Sheikh Dahiru Bauchi RA, ya zama babban malamin a fadin duniya, wanda a yanzu shine mataimakin shugaban masu fatwa na Addini Musulunci a najeriya, kuma khalifan Sheikh Ibrahim Inyass ne a duniya baki daya.
Shehin malamin yana da ya’yan maza da mata mafi yawan su mahaddata Alkur’ani ne tare da dinbin jikokin sama da dari biyu 200, a yanzu yana zaune a garin Bauchi dake arewacin Najeriya.
Allah ya albarkacin rayuwar sa ya kara lafiya da daukaka ya kara masa himma wurin hidimtawa addini Musulunci da darikar Tijjaniyya a fadin duniya. Amiin Yaa ALLAH.
Babangida A. Maina
Tijjaniyya Media News