Takaitaccen Tarihin Marigayi Sheikh Ishaq Rabiu Khadimul Qur’an
TARIHIN KHADIMUL QUR’AN KHALIFA SHEIKH ISHAQ RABI’U DA GUDUNMUWAR GA ADDINI
An haifeshi a gidan Sheikh Muhd Rabi’u Dan Tinki, daya daga Many an Malaman addini a Arewacin Nigeria, ya Shahara da Qur’ani da Ilmi Sheikh Nasiru Kabara Kano na cikin Almajirans
Tun daga Mahaifinsa har Kakansa na 5, duka Gwanayen Qur’an ne Mahaddata, yayi Haddar Qur’ani wajen Mahaifinsa 1936_1942 ya Kuma koyi Larabci da sauran ilmoma
Ya tafi Maiduguri domin kara Karatu, yadawo gida yayi Auren farin, ya sake Komawa Zaria a gidan Mal. Na’iya ya kara karatu Shekaru 2 yazama Malami she karat 1949 yafara koyarwa
Ya fara karanta da Qur’ani da Larabci da Ilmi, da Shekaru 24, a farkon 1950, yafara Kasuwanci da Shekaru 25, koda yake bai daina Karantarwa ba, ya kafa Kamfani 1952 Ishaq Rabiu & Sons
Ya fara da zama dilan UAC na kekunan dinki da littafan addini, a 1958 Kamfabin ya bunkasa, da aka kafa Kaduna Textile yazama babban dila ya zama babban dilan Kamfanin Arewacin Nigeria
Kuma shi da wasu 1963, suka kafa Kano Marchent Trading Company, ya Kuma kafa Kamfanin Dunka kayan sawa, 1970 ya goyi bayan NPN a Jamhriya 2, ta kafa Gwamnati
A 1972, ya kafa Bagauda Textile ya Kuma kafa wasu kananan kamfuna don taimakon mutane da bunkasa tattallin arzikin Kasa yayi Wafati da Shekaru 93 a shekarar 2018, yabar mata 4 da ‘ya’ya 63 da Jikoki masu matukar yawa sosai
SHAHARARSA A NIGERIA DA DUNIYA
Ya Shahara ne da Qur’ani da Khudimarsa kuma ya Shahara a Kasuwanci da Taimakon Jama’a .
Ya kwashe Fiyeda Shekaru 70, Qur’ani na cikin Kansa yana karantashi dare da rana yana bada Sallar Tahajjud dashi yana Khidimar Quran da Makarantarsa da Mahaddata tsawon rayuwarsa
Har ya Gina Jami’ar Qur’an shi kadai, Gadon Maya, ya Gina Masallatan Sallolin Farilla dana Juma’a a wurare da yawa daga cikinsu akwai:
1. Sheikh Muhd Rabi’u Goron Dutse 1983
2. Sheikh Ahmad Tijjani Kofar Mata 1996
3. Sheikh Ibrahim Inyass Gadon Kaya 2008
4. Sheikh Ishaq Rabiu Jakara 2015
5. Sheikh Sharif bn Salim Kwankwasiyya 2019
6. Jami’ur Rasul Kwarin baka Sabuwar Gwandu
Ya Gina Gidaje 60, ya baiwa Mahaddata Wakafi
Ya Tatar da Library ta Mahaifinsa ta littafai fiye da 2000, ya maida fiyeda 5000, ya samu lambobi na yabo a kasa da duniya da yawa
Ya Shuganci Kungiyoyin Addini a Nigeria da wajenta fiyeda 10, bayan Zamowarsa Khalifan Tijjaniya a Nigeria, kuma Shugan Majalisar ta na Shura
Member ne a Majalisar kula da Masallatai ta Duniya, Member ne a Majalisar tsara aiyukan cigaban Musulunci ta duniya, dake Makka, kuma Jagora ne a Munazzamatu Fityanil Islam
Allah ya fada a Qur’an, Wadanda suke karanta Littafin Allah suka tsaida Sallah suka ciyar daga abinda muka arzurtasu bayyane da 6oye suna kwadayin Kasuwanci (da Allah) da babu hasara ( Khalifa yayi wannan da aka fada)
Har Allah yace sai muka gadar da Littafin (Qur’an) ga wadanda muka za6a daga bayinMu ya shiga cikin Za6a66u Fadir 32
A Hadisan Falalar Mahaddata Annabi saw yace
Masu Qur’ani sune Mutanen Allah Ibn Majah
Mafi Alherinku Wanda ya koyi Qur’ani ya koyar (Bukhari, Muslim, Tirmiziy, Nasa’i Abu Daud )
Allah ya daga darajar wasu mutane da Quran, Muslim ( Kamar dai shi Khalifa)
TA FUSKAR TAIMAKON JAMA’A Annabi yace:
Mafi Alherin Mutane Wanda rayuwarsa tayi tsawo aikinsa yayi kyau Tirmiziy
Wanda yasamu damar taimakon Dan Uwansa to ya taimakeshi Muslim
Idan Adam ya mutum aikinsa ya tsaya sai dai Abu 3, duk ya samesu, 1, Sadaka mai gudana, 2, Da mai masa Addu’a, 3, Ilmi daya koyar
Abubuwan da yawa kamar Daukar nauyin Dalibai suyi karatu a Jami’o’in Madina, Sudan, Niger, Nigeria da sauran su Kula da Marayu, Marasa lafiya, ‘Yan gidan Yari, Gajiyayyu, Tsoffi
Allah Ina rokonKa da Sunayenka da Siffofinka ka Kara Gafara da RahmarSa da kusanci da yarda ga Khalifa Ishaq Rabiu Khadimul Qurani
don Girman Annabi saww da Qurani
Ya Razzaku, Ya Wahhabu Ya Mu’udi, Ya Barru Ya Kareemu Kai mana baiwar irin Arzikinsa da irin Aiyukansa na Alheri don mu rabauta muma.
Annabi saww yayi Gaskiya Madallah da Duniya ta kwarai ga Mutumin Kirki, kamar dai Maulana Sheikh KHALIFA Ishaq Khadimul Qur’an RTA.
Abdulhakeem Ahmad Ya’akub Gusau