Takaitaccen Tarihin Sheikh Ahmadu Tijjani RA (Cikamakin Waliyai) Kashi Na Bakwai 7

CIKAMAKIN WALIYAI (7)

 

TAFIYAR SA ZUWA FAS

 

Hijira tana shekara 1171 (1757/58 Miladiyya) Shehu Ahmadu Tijjani RTA ya cirata daga Aini Madhi zuwa birnin Fas/Fez, a lokacin shekarun sa 21. Wannan birni ya kasance babban birni mai dauke da tarihin malamai da waliyai shahararru a ƙasar Morocco, musamman saboda babban jami’ar ilimin nan da ake kira “Masjidil Ƙarawin/Jami’atul Ƙarawin” wanda wata baƙuraishiya mai suna Fatima Alfihiri ta assasa a shekarar 857/858 (miladiyya).

 

Shehu Tijjani ya ziyarci waliyan dake cikin fas domin neman albarkar su, sannan ya ilimantu sosai daga abinda ake koyarwa a jami’ar da ma wasu masallatai da zawiyoyi a fas. Shehu Tijjani bai taɓa gajiya da sha’anin ilimi ba, yana cewa ilimi ya rabu kashi hudu kamar haka:

 

1. Ilimi mai karfafa zuciya, wato ilimin fikihu.

2. Ilimi mai sa a kwaɗaitu da ilimi, wato ilimin nahawu da ire-iren shi.

3. Ilimi mai sa a fahimci rayuwar duniya, shine ilimin tarihi da abinda ya shafe shi.

4. Ilimi mai raya zuciya, wato ilimin hadisi da duk abinda aka samo daga gareshi.

Shiyasa Shehu Tijjani yake son abinda ya shafi hadisi sosai.

 

A zaman sa a fas, ya mu’amalantu da waliyai guda shida, daga cikin su akwai Sheikh Ɗayyib ɗan Muhammad RTA wanda ya bashi Ɗariqar Wazaniyya wanda ake yiwa lakabi da “Ɗariqar Ɗayyibiyya Shazaliyya”, asalin darikar daga Jazuliyya ne, shehin yaso ya ƙaddamar da Shehu Tijjani amma Shehu Tijjani bai yarda ba.

 

Sannan ya mu’amalantu da Sheikh Ahmad Saƙ-li RTA wanda ya kasance babban ƙuɗubi a Ɗariƙar Halwatiyya amma ance shehu Tijjani bai karɓi Darikar ba, wasu kuma sunce ya karɓa. Sannan ya karɓi Ɗariƙar Ƙadiriyya a wurin mukaddamin ta na wancan lokacin a fas, kuma ya karbi Ɗarikar Nasiriyya a wurin Sheikh Muhammad ɗan Abdullahi RTA wanda ake kira “Rifi”. Kuma ya karbi Ɗariƙar Sheikh Ahmad Habib RTA wanda ake kira “Al Gamari” daga wurin muqaddamin Ɗarikar na wancan lokacin, sannan shehin Ɗariƙar wato Sheikh Ahmad ya bayyana ga Shehu Tijjani a cikin mafarki ya bashi wani ismul A’azam.

 

✍️ Sidi Sadauki

Share

Back to top button