Masha’Allah: Sayyadi Akibu Jikan Sheikh Ibrahim Inyass Ya Samu Kubuta Daga Hannun Yan Kidnapped.

MADALLAH DA SHAKAR ISKAR ‘YANCI.

 

Ko ayayin da na soma cin karo da labarin cewa anyi garkuwa dashi (SAYYADI AQIBU JIKAN SHEIKH IBRAHIM INYASS (R.T.A), zuciya tayi matukar sosuwa sosai, naso yin rubutu domin jajantawa ‘yan uwa tare da karfafawa akan yin Addu’a, amma sai wani tunani ya zomin a zuciya cewa “Sakin rubutu a Midiya, tamkar tashin hayakine, yakan iya zuwa inda kake zato harma inda baka zato” muddin labari ra riski ‘yan Kidnappings sukasan kima da darajar wanda suke garkuwa dashi garemu masoya Shehu Ibrahim da zuriyarsa, to lallai farashin da zasu daura masa zai matukar yawa, wanda hakan yasa ni da masu irin wannan tunani nawa muka hadiye kalmominmu a zuciya, muka sirrantu da yi masa addu’a a zahiri da badininmu.

 

Abin farin ciki ne babba, samun kubutowarsa a wannan lokaci, muna rokon ALLAH yasa wannan imtihanin ya zamo sila na kara daukaka da hauhawar matsayinsa a wajen ALLAH, ya zamo mabudine ga kofofin taraqi.

 

ALLAH YA KUBUTAR DA DUKKANIN WADANDA AKE GARKUWA DASU, YA AMINTAR DA WADANDA SUKE CIKIN HALI NA TSORO, KUMA YA BAIWA KASARMU ZAMAN LAFIYA DA KWANCIYAR HANKALI. AMIIN

 

Daga: Muhammad Usman Gashua.

Share

Back to top button