Takaitaccen Tarihin Sheikh Ahmadu Tijjani RA Cikamakin Waliyai Kashi Na Goma Sha Biyu (12).

CIKAMAKIN WALIYAI (12)

 

 

SAMUWAR DARIKAR TIJJANIYYA

 

A Tilmisan Shehu Tijjani ya haɗu da ɗaya daga cikin manyan almajiran sa, wato Sidi Muhammadul Mishiri RTA. Shehu Tijjani ya bashi Ɗariqar khalwatiyya sannan ya umarce shi ya dinga jagorantar khamsus salawatu domin Shehu Tijjani baya son yin kowacce irin jagoranci saboda tsananin ƙas-ƙas da kan sa.

 

Jama’a suna zuwa gun Shehu Tijjani domin neman iznin kasancewar sa jagoran su, amma shi bayan ya basu Ɗarikar Khalwatiyya sai yace musu “ni daku abokai ne, ban fi ku ba ballantana in zama shehin ku”.

 

Hijira tana 1191 Shehu Tijjani RTA ya kama hanyar zuwa Fas domin ziyartar raudar Maulaya Idris, sai ya bi ta Ujda, a nan ya haɗu da babban almajirin sa wato Sidi Aliyu Harazumi RTA a cikin ayarin matafiya. Bayan kwana kaɗan sai Shehu Tijjani ya nunawa Sidi Aliyu Harazumi karama ta hanyar tuna masa mafarkin da yayi da Shehu Tijjani tun shekaru biyu da suka wuce alhalin ya manta, Sidi Aliy Harazumi yace Alhamdulillah wannan ranar nake jira kuma tazo, Maulana gani a hannun ka kayi yadda kaso.

 

Bayan Shehu Tijjani ya dawo Tilmisan sai ya cigaba da ilimantarwa da tarbiyantar da al’umma, amma saboda zalunci da hantarar bayin Allah da wani kwamandan yaƙi yake yiwa mutane, hijira tana da shekara 1196 shehu Tijjani ya bar tilmisan zuwa garin “Abu Samguna”. Wannan garin ya samo sunan sa ne daga wani baban Waliyyi wanda ake kira Abu Samguna, kuma an tabbatar Shehu Tijjani shine Waliyyi na arba’in da ya zauna a garin.

 

A garin Abu Samguna, 17 ga watan Safar 1196H, Shehu Ahmadu Tijjani RTA ya samu kololuwar buɗi (Fat-hul Akbar) domin ya ga Annabi SAW ido da ido ba a bacci ba, dama ya saba ganin sa a haka amma wannan ganin ya girmi sauran saboda yanayin ganin da abinda ganin ya ƙunsa, wato Annabi SAW ya umarce shi da ya saki zikirin kowacce Ɗarika, daga wannan ranar shi (Annabi) da kansa ne shehin sa, shi zai dinga yi masa madadi, babu wani waliyyi mai iko dashi, sannan ya bashi izinin yin Astagfirullah 100, Salatin Fatihi 100 kullum, kuma yayi masa iznin bayar dasu ga duk wanda ya nema tareda sharuɗɗan da za a kiyaye,

 

Sannan Annabi SAW yayi masa bushara cewa “Duk wanda ya karɓa daga gareka, da shi da iyalin shi da iyayen shi da masoyan shi za su shiga aljanna babu hisabi balle azaba, zasu kasance tare dani a “Illiyyina”, kaine mai ceto ga duk wanda ya bika, ka rike zikirorin nan da kyau ba tareda halwa ko wani jiyar da jiki wahala ba har abinda aka yi maka alkawari (ƙuɗbabniyyatil uzma) ya tabbata”.

 

Bayan shekaru hudu wato 1200H, Annabi ya sake bayyana gareshi ya cika masa da La ilaha illallahu 100 da sauran abubuwa wayanda Ɗarikar Tijjaniyya ta ƙunsa a yau. A shekarar nan ne kuma Shehu Assammani ya rasu, don haka jama’a suka karkato gaba daya ga Shehu Tijjani domin neman ilimi da saduwa da Allah ta hannun sa, suna zuwa masa da kyaututtuka na kudi da dukiya irin su raƙuma.

 

RANAR LARABA 21 AUGUST 2024 SHINE DAIDAI DA 17 SAFAR 1446, DARIKAR TIJJANIYYA TA CIKA SHEKARU DARI BIYU DA HAMSIN (250 YEARS) DA SAMUWA.

 

Alhamdulillah Masha’Allah

 

✍️ Sidi Sadauki

Share

Back to top button