TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA ASHIRIN DA UKU (23)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 23

 

YAƘIN BADAR

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Ranar Juma’a 18 ga watan Ramadan bayan hijira da Shekara 2 ne akayi yaƙin Badar. Wanda shine ya Zama yaki na Farko cikin tarihin Addinin Musulunci.

 

Annabi Muhammad (SAW) ya fita tareda Sahabbai 313, sun fita cikin Shirin yaki domin su kwace kayaki, da Dukiyoyinsu da aka kwace musu yayin barinsu Makka, yayinda Fataken (‘yan Kasuwa) Quraishawa suke hanyarsu ta Dawowa daga Sham (Syria) domin kasuwanci.

 

Kafiren Makka dajin labarin abunda ke faruwa sukayi Kiran gaggawa domin ayi gangami a fita yakin kare Dukiya da Mutanensu. Manyan Masu kudi cikin Kafiren Makka sune suka dauki nauyin duk wasu wadanda zasu fita wannan Yakin.

 

Kimanin Kafiren Makka dubu dayane (1,000) suka fita domin yaƙin. Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa 313 ne kadai da Bangaren Musulmai.

 

Fara yaki keda wuya, sai Allah (SWT) ya bawa Annabinsa Nasara yakuma durkusar da Makiyan Addininsa. Kafurai 70 aka kashe a Wannan Yaƙin ciki harda Abu-Jahal, aka kama Fursinonin yaki 70. cikin ikon Allah Musulmai 14 ne sukayi Shahada.

 

Annabi Muhammad (SAW) yayi musu umarni cewa karsu cutar da Fursinonin yaki, (Kafiren da aka kama a wajen yaƙi), Wanda keda Kudi fansa a cikin su za’a fansheshi Kimanin Dirhami dubu Hudu 4,000, wadanda Basuda komai kuma, Idan sun yarda zasu koyar da Yara Goma 10 a Madina Karatun Larabarci da dabarun Yaki to zasu fanshi kansu.

 

Wannan a takaice kenan, yadda Yaƙin Badar Babba ya kasance. Allah ya Kara mana lafiya da Kaunar Annabi Muhammad (SAW). Allah y la bamu imani mai daurewa da himma marar yankewa Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Back to top button