MANZON ALLAH

  • GAMSASSUN HUJJOJI NA HADISI MASU NUNA CEWA IYAYEN ANNABI (SAW) ‘YAN ALJANNA NE.

    DALILAI NA HADISI MASU NUNA CEWA IYAYEN ANNABI (SAW) ‘YAN ALJANNA NE.

     

    Sheikh Halliru Abdullahi Maraya Kaduna.

     

    Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) da Ya ba mu dama , a jiya , muka gabatar da wasu daga cikin dalilai na hankali masu nuna cewa iyayen Manzon Allah (SAW) ba ‘yan wuta ba ne . Allah (SWT) Ya kara masu (AS) rahama da yarda. Insha’Allah, yau, zamu kawo wasu dalilai na Hadisin Manzon Allah (SAW) masu nuna haka Allah (SWT) Ya kara wa ManzonSa (SAW) matsayi da alfarma. Akwai dalilai na Hadisin Manzon Allah (SAW) da suke nuna cewa iyayensa (AS) muminai ne , ‘yan Aljanna . Daga ciki akwai:

     

    i. Waathilah Ibnu Asqa’i (RA) yace: Manzon Allah (SAW) ya ce “Lallai Allah Ya zabi Ismaa’iil (AS) daga cikin ‘ya’yan Ibraahiim (AS) kuma Ya zabi ‘ya’yan Kinaanah daga cikin ‘ya’yan Isma’iil (AS), kuma Ya zabi Quraysh daga cikin ‘ya’yan Kinaanah , kuma Ya zabi ‘ya’yan Haashim daga cikin Quraysh , sannan (daga karshe) Ya zabe ni daga cikin ‘ya’yan Haashim .”Manazarta : Sahiihu Muslim .

     

    ABUN DA HADISIN KE NUNAWA:

     

    Wannan Hadisi yana nuna cewa acikin kowace Jama’a , tun daga Annabi Ibraahiim (AS) har zuwa lokacin haihuwar Manzon Allah (SAW) , Allah (SWT) Yana zaben mutane ne mafifita a wurinSa (SWT), sannan Ya sa Manzon Allah (SAW) a tsatsonsu. A takaice, mai lafiyayyen hankali zai fahimta daga wannan Hadisi cewa iyayen Manzon Allah (SAW), tun daga Annabi Ibraahiim (AS) zuwa iyayensa na haihuwa, zababbu ne a wurin Allah (SWT). Kafirai kuwa ba zababbu ba ne a wurin Allah (SWT) . Saboda haka, Hadisin ya nuna cewa Abdul-Laahi (AS) da Aaminatu (AS) , iyayen Manzon Allah (SAW) , zababbu ne a wurin Allah (SWT) ba ‘yan wuta ba.

     

    ii. Sayyidunaa ‘Aliyyu (RA) ya ce : Manzon Allah (SAW) ya ce : ” An haife ni ne ta hanyar aure , ba a fitar da ni ba ta tsatson mazinaci tun daga Aadam (AS) har zuwa lokacin da mahaifina da mahaifiyata suka haife ni .”Manazarta : Imam At- Tabaraaniyyu , Mu’jamul-awsad.

     

    ABUNDA HADISIN KE NUNAWA:

     

    Wannan Hadisi na nuna cewa iyayen Manzon Allah (SAW) , Abdul-Laahi da Aaminatu (AS) , ko zina basu taba yi ba , balle kafirci.

     

    Manzon Allah (SAW) na alfahari da cewa iyayensa (AS) ko zina basu taba yi ba . Wato cikakkun mutane ne na kwarai. Mu sani , kafirci shi ne sabon Allah (SWT) mafi muni da girma. Iyayensa (AS) ba kafirai ba ne , da kafirai ne , da bai yi alfahari da cewa ko zina basu taba yi ba.

     

    Domin da kafirai ne , da kenan sun aikata laifin da ya fi zina girma sosai . Saboda haka , da bai yi alfahari ba da rashin yin zinarsu. Misali: Mutum ne iyayensa ba sa shan taba , amma suna shan koken (Cocaine) , dan Allah zai iya alfahari saboda cewa iyayensa ba sa shan taba ? A nan zan tsaya yau. In sha’Allah, gobe ko jibi , zan yi magana a game da ainihin mahaifin Annabi Ibraahiim (AS) , wato daya daga cikin kakannin Manzon Allah (SAW) . In sha’Allah , zamu ji waye hakikanin mahaifinsa.

     

    Daga baya kuma , in sha’Allah , sai mu je kotun koli , wato Alqur’ani Mai girma , a game da cewa iyayen Manzon Allah (SAW) ba yan wuta ba ne kamar yadda wasu ke tallatawa . Allah Ya kiyaye ! In sha’Allah , daga karshe , sai mu rufe da yin magana a game da hujjojin da masu wannan mummunar maganar suke amfani da su domin a yarda da wannan magana tasu mai munin gaske . Allah (SWT) Ya kara wa Manzon Allah (SAW) , alayensa (AS) , da

    sahabbansa (RA) matsayi da yarda. Mu kuma , Allah (SWT) Ya kara mana soyayyarsu.

     

    Allah Ya kara wa kasarmu, Nijeriya , arziki da zaman lafiya. Duk wadannan, Allah Ya amsa mana saboda alfarmar Manzon Allah (SAW). Amiiiin Yaa ALLAH

  • A Bisa Hankali Da Al’adar Zamantakewa JINI Ko FITSARI/BAWALI Najasa Ne, To Amma Al’amarin Ba Haka Yake Ba, Akan Na MANZON ALLAH(S.A.W).

    JINI Ko BAWALI/FITSARI;

     

    A Bisa Hankali Da Al’adar Zamantakewa JINI Ko FITSARI/BAWALI Najasa Ne (Musamman a Duniyar Musulmai An Tabbatar Da Cewa; JINI Ko FITSARI Da BAWALI Najasa Ne),

     

    Kuma Ta Fuskar Malaman Lafiya (Likitoci) Guba Ne, Na Kowa Haka Yake,

     

    To Amma Al’amarin Ba Haka Yake Ba, Akan Na MANZON ALLAH(S.A.W), JININSA Da BAWALINSA Ba Najasa Bane,

     

    Saboda Me???

     

    Saboda Suna Da Dangane/Alaqa Da MANZON ALLAH(S.A.W), Hasalima An Sha Su An Samu Lafiya, An Warke Sumul,

     

    Karatun Da Nake So Na Fitar Anan Shi Ne; Duk Abinda Yake Da Dangane/Alaqa Da MANZON ALLAH(S.A.W), To Yafi ‘Karfin Kushe Ko Muzantawa Komai ‘Kankantarsa, Ko Rashin Tsarkinsa a Gare Mu, Don Haka Ne;

     

    IYAYEN MANZON ALLAH(S.A.W),

    IYALAN MANZON ALLAH(S.A.W),

    MATAN MANZON ALLAH(S.A.W),

    SAHABBAN MANZON ALLAH(S.A.W),

    KAYAN MANZON ALLAH(S.A.W),

    DABBOBIN MANZON ALLAH(S.A.W),

    GARIN MANZON ALLAH(S.A.W),

     

    Da Sauransu,

     

    Duk Sun Fi ‘Karfin a Ta6a Su, Ko a Muzanta Su Saboda Suna Da Nasaba Ta Kai Tsaye Da MANZON ALLAH(S.A.W).

     

    Don Haka Masu Ta6a Mutumcin IYAYEN ANNABI(S.A.W) Sai Ku Shafawa Kanku Ruwa, Ku Kiyaye.

     

    Kun Ji Dai FITSARI/BAWALI Ko JININ MANZON ALLAH(S.A.W) Ma Yafi ‘Karfin Muzantawa Balantana IYAYEN ANNABI (S.A.W).

     

    Ku Ji Abinda QADHI IYAD Ya Ce;

     

    “KO FITSARIN DABBAR DA ANNABI (S.A.W) YAKE HAWA, IDAN MUTUM YA CE FITSARIN WARI YAKE, TO HUKUNCIN SHI KISA NE!”

     

    – (QADHI-IYAD MAI ASHIFAH SHI YA RUWAITO HAKAN).

     

    ALLAH KA ‘KARA TSARE MANA IMANINMU DAGA RUDANIN ZAMANI, YA ‘KARA MANA ‘KAUNAR SAYYIDUL-WUJUDI (S.A.W) AMEEEN

  • SIRRIN GANIN ANNABI SAW: Idan Kasa Son Ganin Manzon Allah SAW Ka Karanta Rubutun…

    SIRRIN GANIN ANNABI SAW

     

    Munyi alqawarin kawo fassarar faidhul Ahmadiy na haihuwar Annabi SAW, kuma mun kawo shi cikin sigar tambayar yan’uwa da bada tukuici ga wanda yayi nasarar bada amsa daidai, sannan munyi rubutu mai taken MAULIDIN ANNABI daga na daya zuwa na hudu. Toh abinda yayi saura shine MU’IJIZAR ANNABI da kuma SIRRIN GANIN SA ido da ido ko a mafarki, sirrin zan bayar yanzu da iznin shehu Abulfathi RTA.

     

    Amma kafin in bada sirrin, ya kamata yan’uwa su san rabe-raben dake cikin ganin Annabi SAW. Owaisul Qarni yace sahabbai basu ga/san Annabi ba, abubakar ne kawai yayi kokarin ganin/sanin inuwar Annabi SAW. Magana yayi musu da harshen zati, kuma ishara ne garemu na baya akan muyi kokarin riskar ma’arifa (haqiqa) cikin lamarin Allah da Annabi SAW domin muyi gam da katar da qwayar shari’a ba bawo ba.

     

    Zan bayar da sirrin bisa matakin musulunci guda uku, wato ISLAM (Musulmi), IMAN (Mumini) da kuma IHSAN (Arifi), duk wani masoyin Annabi yana cikin daya daga wannan muqamin.

     

    1. Idan kai musulmi ne amma baka karbi dariqar tijjaniya ba, ga sirrin ganin Annabi SAW. Ranar lahadi zaka karanta ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN WA SALLIM sau 92 bayan kowace sallar farilla, sannan in zaka kwanta kayi salatin sau 1,111, haka zaka yi har kwana 7, yayin kwanciyar ka, ka shagala da tunanin kyawawar halaye da siffofin Annabi da ka sani, a haka har bacci ya kwashe ka, da iznin Allah zaka ga Annabi a mafarki ko ido da ido kafin kwana bakwai din nan, gwargwadon abinda Allah ya nufe ka da samu daga falalar sa.

     

    2. Idan kai batijjane ne amma baka yi tarbiya ba, ga sirrin ganin Annabi SAW. Zaka lazumci karanta salatul fatihi sau 535 bayan sallar asubah da sallar la’asar, in zaka kwanta kayi jauharatul kamali kafa 12, amma da alwalla kuma a wuri mai tsarki, kayi haka har tsawon kwana 7 ko 21 ko 41, zaka sadu da Annabi, zaka samu shirya zuwa ga sahihin shehin da zai maka tarbiya, zaka samu saduwa (wusuli) yayin tarbiyar cikin sauqi.

     

    3. Idan kayi tarbiyatul azkar, toh aikin nan kwana 41 zaka yi, zaka fara ranar lahadi bayan kowacce sallar farilla kamar haka:

    A. Sallar Asuba: ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN ALFATIHI LIMA UGLIQA sau 1000.

     

    B. Sallar Azahar: ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN ALKATIMI LIMA SABAQA sau 1000.

     

    C. Sallar La’asar: ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN NASIRIL HAQQI BIL HAQQI sau 1000.

     

    D. Sallar Magriba: ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN ALHADI ILA SIRADIKAL MUSTAQEEM sau 1000.

     

    E. Sallar Isha’i: ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN WA ALA ALIHI HAQQA QADRIHI WA MIQDARIHIL AZEEM sau 1000.

     

    wanda duk yayi wannan zai samu FATHUL AKBAR wanda shine karshen kyautar da batijjane wanda yayi tarbiya zai samu daga Allah.

     

    Ina tawassali da soyayyar da kuke yiwa Annabi SAW, in samu yarda da soyayyar shehu Abulfathi gami da hidimta masa hissan wa ma’anan, Alfarmar Maulana sayyidina Rasulillah SAW. Amiin

     

    ✍Sidi Sadauki

Back to top button