Yau Shekara 123 Da Haihuwar Sheikh Ibrahim Inyass Al-khaulahi (R.A).

Yau Shekara 123 Da Haihuwar Sheikh Ibrahim Inyass Al-khaulahi (R.A).

 

An Haifi Sheikh Ibrahim INyass A Wata Alqarya Da Ake Kira Daiba Dake Cikin Kasar Senegal, Bayan Sallar La’asar Ranar Alkhamis 8/Nov/1900 Wanda Yayi Dai-dai da 15/Rajab 1318Ah.

 

Sheikh Ibrahim Inyass Ya Tashi Karkashin kulawar Mahaifinsa Inda Ya Haddace Alqur’Ani da wasu fannona na Ilimi, shehu yazama cikakken malami a kowanne Fanni Koh Da Yakai Shekara Ishirin Da Daya A Duniya.

 

Shehu ya fara rubuta Littafin Ruhul -Adab yana dan shekaru ashirin da daya, ya rubuta Littafi 75 Duka a rayuwar sa, shehu ya kare a cikin soyayyar ma’aiki Tare da Tsamo Halitta daga ‘bata zuwa shiriya, shehu ya watsa Addini a fad’in duniya sannan ya shigar da mutane da dama a Darikar Tijjaniyya, shehu yayi Tarbiyyar malamai da yawa har sukayi Usuli suka sadu da Allah.

 

Shehu yakarar da rayuwar sa cikin hidima ga Allah da manzon Allah, Shehu yayi Qafatii 26/July 1975 A Asibitin Thomas Kasar Landan Dake Babban Birnin “UK”.

 

Allah yakara masa karamar barzahu, Allah ya jaddada Rahma gareshi, Allah yabamu Albarkarsu Alfarmar manzon allah (S A W). Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button