MAULUD

  • Wata Rana An Tambayi Maulana Sheikh Ibrahim Inyass (Ra) Menene Hujjan Yin MAULUD ?

    Farfesa Ibrahim Maqari Yana Cewa;

     

    Wata rana an tambayi Maulana Sheikh Ibrahim Inyass (Ra) menene hujjan yin MAULUD ?

     

    Sai Shehu yace rashin Hujja Maulidi shine ya kawo hujjan mu na yin mauludin Domin akwai Abunda yafi Qarfin hujja Shehu yace baka ga duk Qur’ani, ba inda Allah yacema UWA ta so DAN ta ba ?

     

    Ai Allah bai cema UWA ta so DAN taba, saboda bata bukata sai ance mata ta so shi zata so shi. Domin Allah ya riga ya shuka son DAN acikin UWAN, Amma shi DAN da a kasan zai iya Qin biyayya baka ga wuri daban daban Allah yake umartarsa da bin iyaye ba?

     

    SHARHI

     

    PROFESSOR IBRAHIM MAQARI yana cewa: Watarana an taba haduwa da wata mata aka nunamata wani malami “imamul Faharrazi” aka ce mata kinga malamin can zai iya baki Hujja dubu akan samuwan Allah

     

    Sai matan tace “Allah sarki miskini!

     

    Ai yana da shakka dubu ne a zuciyarshi shiyasa har zai iya samo hujja dubu in ba haka ba ya za’ayi mutum, in ba mahaukaci ba yadauko “touch light” da rana kuma yace wai yana neman Rana.

     

    Duk girman hujja ai bata kai “touch light” rana tare da ubangiji ba, Allah da yakira kansa “Azzahiru” kuma yake bukatan wata hujja tazo ta bayyana dashi ? Ai Lamarin Akwai Abun dubawa

     

    Allah yakarawa PROFESSOR lafiya da fahimta bijahi S.A.W. Amiin Yaa Allah

  • MANZON ALLAH (S.A.W) Ba Irinmu Bane, Domin Da Kansa Yake Cewa.. ‘Ayyukum Ka Hai’atiy. Inji Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari

    SHEIKH (Prof.) IBRAHIM AHMAD MAQARY (R) Yana Cewa:

     

    “MANZON ALLAH (S.A.W) Ba Irinmu Bane, Domin Da Kansa Yake Cewa… ‘Ayyukum Ka Hai’atiy???

     

    Ma’ana: Wanene Ke Da Structure Irin Tawa???”.

     

    To Kuma Gaba ‘Daya Wadanda Suka Kafirce Ma Annabawansu Sun Kafirce Ne Saboda Sun ‘Dauka Kuma Sun Ce Annabinsu Mutum Ne Kamarsu…”,

     

    ‘Yan’uwa Mu Kula… A Kula… ANNABI Ba Irinmu Bane.. Halitta Ne Wanda a Hadisin Bukhari Aka Ruwaito Cewa:

     

    Lokacin Da SAYYIDUNA ALI(R.A) Ya Hau Kan Kafadarsa Lokacin FATHU MAKKAH Sai Da Ya Ga Kamar Zai Iya ‘Dauko Taurarin Sama,

     

    Ku Duba Tsawon Ka’aba Amma SAYYIDUNA ALI (R.A) Yana Hawa Kafadan ANNABI (S.A.W) Ya Ciro Wadannan Gumakan Kuma Ka’aba Kowa Ya San Tsawonta Dai… A Nutsu/Kula Dai”.

     

    LA ILAHA ILLALLAH…

     

    ALLAH YA ‘KARA TSARE MANA IMANINMU, YA ‘KARA MANA ‘KAUNAR SAYYIDUL-WUJUDI (S.A.W) AMEEEN

  • IBLISA” SHINE SHUGABAN MAZHABAR MAKIYA MAULUDIN MANZON ALLAH (S.A.W)..?

    KO KASAN DA CEWA “IBLISA” SHINE SHUGABAN MAZHABAR MAKIYA MAULUDIN MANZON ALLAH (S.A.W)..?

     

    Imam Ibn Kathir ya kawo Hadisi a littafinsa Albidaya Wannihaya, Mujalladi na 2 Shafi na 166, kamar haka:-

     

    أن إبليس رن أربع رنات حين لعن وحين أهبط وحين ولد رسول الله صلى الله عليه وسلم وحين أنزلت الفاتحة

     

    Ma’ana: Lallai ne Iblisa yayi kururuwar kokayya sau hudu, Lokacin da aka la’anceshi, da lokacin da aka fitar da shi (Daga Aljannah) da lokacin da aka Haifi MANZON ALLAH (S.A.W) da kuma lolacin da aka sauke Fatiha.

     

    A rike lissafin

     

    Duk yadda aka kai ga chanja zance da boyewa gaskiyar da take bayyana shi ne, nuna bakin ciki akan nuna farin ciki da haifuwar MANZON ALLAH (S.A.W) bakin ciki ne ga samuwarsa (S.A.W), tunda a yau ta kai har bomb ake tadawa cikin taron Masu Mauludi a wata kasa, a yayin da yan uwansu na nan suke farin ciki da hakan.

     

    IDAN HAR YANA DAGA CIKIN ABABEN DA SUKA SANYA IBLISA KUKA DA KURURUWA, BAKIN CIKI DA HAIFUWAR MANZON ALLAH (S.A.W), TO ANYA KUWA MASU KURURUWA YAU AKAN KIYAYYAR FARIN CIKI DA HAIFUWARSA (S.A.W) BA SUNE HAKIKANIN YAN MAZHABIN SHAIDAN BA…?

     

    Kar kayi mamaki dan uwa, domin ANNABI (S.A.W) ya fadi a hadisi sahihi cewa “Kahon Shaidan zai bayyana a Najadu” Malamai sunyi ittifaki akan wannan kahon Shaidan din shine “IBNU ABDULWAHAB ANNAJADI”.

     

    Shine Malami guda a tarihin Musulunci da yake yaki da yin Mauludi, kuma Almajiransa (WAHABIYAWA) suka sunnatu akan hakan, domin shine wanda ya aiwatar da ta’addanci akan Sharifai a Makkah da Madina ya karkashesu, ya karbe jagoranci daga garesu ya dankawa Ahli Sa’ud, kuma ya hani da ko a bayan kiran Sallah kada ayi salati ga MANZON ALLAH (S.A.W), kuma shine yake taya Shaidan aiki wajen son ganin an kira Musulmi da sunan Kafirai, Mushrikai, Yan Bidi’a, domin adadin yan wuta ya linka yan Aljannah a Al’ummar MANZON ALLAH (S.A.W) kamar dai yadda Almajiransa ke yin da’awa a salon hakan a yau.

     

    SABODA HAKA A TAKAICE DUK WANDA KAGA YANA KIN MAULUDI A YAU DAYAN BIYU NE, KO WANDA AKA RIBATA CIKIN JAHILCI, KO KUMA WANDA YAKE TAYA MAI GIDANSHI IBLISA BAKIN CIKI DA SAMUWAR MANZON ALLAH (S.A.W).

     

    ALLAH KA TSARE MU DA BIN TAFARKIN SHAIDAN DA AYARINSA.

     

    Daga: Muhamad Usman Gashua

  • MASHA’ALLAH; Annabi Muhammad (SAW) Shi Ya Fara Yin Maulidi – Cewar Sheikh Ahmadu Zaria.

    Annabi Muhammad (SAW) Shi Ya Fara Yin Maulidi – Cewar Sheikh Ahmadu Zariya.

     

    Daga Idiris M Usman (Daddy Big’ja) Zariya

     

    Shahararren Malamin Addinin Musulunci Mai Suna Ahmadu Madahun Nabiyi Zariya ya bayyana cewa ƙago wani Sabon Abu a cikin Musulunci bai taɓa zama haramun ba face halastaccen Abune.”

     

    Shehin Malamin ya ƙara da cewa Annabi Shine ya fara yin Maulidi domin yazo a Hadisai kuma Allah bai hana Maulidi ba duba da bai zo a Al-Qur’ani cewa abune Haramun.

     

    Bugu da ƙari Sheikh Madahu ya ci gaba da cewa Allah (SWA) ya kawo ƙissan Maulidin Annabi Isah (AS) dakansa Acikin Al-Qur’ani bare kuma dan Musulmi suna kwaikwayo da Hakan sai ya zama haramtaccen Abu ? Don sun yi Maulidin Annabi Muhammadu (SAW).

     

    Allah ya barmu da soyayyan Annabi ﷺ. Amiin

  • Bikin Takutaha A Kano Ya Cika Shekaru 700 Da Fara Gudanarwa.

    Bikin Takutaha A Kano ya cika Shekaru 700 biki ne na murnar yin nasarar rushe tsunburbura da yai dai dai da ranar Sunan manzon Allah Sallallahu Alaihiwasallam.

     

    ASALIN BIKIN TAKUTAHA A KANO

     

    TUN DAGA ZAMANIN SARKIN KANO ALI YAJI DAN TSAMIYA.

     

    A duk 19 ga watan Rabiul Awwal, a jihar Kano kanawa suna gudanar da wani bikin Wanda ake Kira Takutaha.

     

    Shin menene Asalin Tarihin sa ? Menene Alakar Bikin da Addinin musulunci ?

     

    A wata shekara zamanin sarkin Kano Yaji dan Tsamiya, wasu malaman Wangarawa karkashin jagorancin sheikh AbdurRahman Zaiti suka zo, Kano, baya ga musulunci da kuma kasuwanci, suna da dabarun yaki da baa san da su ba a Kano. Bagaudawa suka karbi musulunci, hannun su, su kuma su taimaka musu don su yaki abokan gabarsu. Kwana daya da zuwansu Sarkin Kano Yaji ya karbi musulunci, ya kuma canjawa kansa suna zuwa Ali. Wanda hakan ke nuna, cewa , shirin yaki zaayi, domin ana cewa Ali bin Abu Talib shine sarkin yakin manzon Allah (saw). Kafin Ali yaji ya musulunta akwai musulmai a Kano saidai basu kai ga kafa mulki ba

     

    A farkon watan Rabiul Awwal na wannan shekara, ne Yaji ya tara dukkan maguzawa, ya kuma karanta musu dokar-ta-baci. Inda yace musu

     

    “Ku sani, daga yau, komai tsakanina daku, sai yaki da tsinin mashi, ba yaudara, bawani boye boye, domin ba mayaudari sai matsoraci, ku shirya gani nan zuwa gareku ko ku karɓi Addinin Musulunci kafin lokacin anyi masu wa’azi suka butulce”

     

    Mataki biyu suka dauka, na farko sunyi kokarin bada cin hanci ga Sarki Yaji, amma yaki karba, yace a maida musu baya so. Na biyu, sai suka koma ga Tsumburbura, domin neman nasara, amma ta gaya musu, cewa wannan yaki ba nasara, domin lokacin karshen addininsu a kasar Kano yazo.

     

    Acikin watan dai, rundunar musulmi suka fuskanci, rundunar maguzawa, a gefen Dutsen Dala, inda suka hadu, aka gwabza. A wannan lokacin ne, Jarmai Bajere ya samu nasarar Kutsa kai cikin shigifar Tsumburbura, inda ya samu wani halitta na tsaye, rike da maciji a hannunsa, ya daga mashi ya bugawa halittar nan, tayi kuwwa ta fito a guje. Nan da nan suka bita, inda ta nufi kofar ruwa, ta fada cikin ruwan Dankwai. Wannan Shi ya kawo karshen Tsumburbura, da kuma addinin maguzawa a garin Kano.

     

    Samuwar wannan Nasara, ba karamin abu bane a wurin musulman Kano. Wanda aka shafe sama da shekaru 100 ana nema. A dalilin haka ne, ya sanya musulman kanawa duk shekara, sukan taru su hau Dutsen Dala domin tunawa da wannan nasara da musulunci yayi akan Maguzanci. Su nunawa duniya cewa, addinin Allah yau ya shafe addinin kafirai. Domin kafin zuwan musulunci, ba mai hawa Dala in ba Babban limamin addinin ba. Amma zuwan musulunci, yanzu kowa ma sai ya hau, ya yi kashi ma aka. Wannan shine dalilin da ya sanya ake takutaha a duk shekara a Kano.

     

    MENENE MA’ANAR KALMAR TAKUTAHA ?

     

    An sha kai-kawo a tsakanin masana game da ma’ana ko asalin wannan kalma ta takutaha. Wannan ce ta sa aka sami mabambantan ra’ayoyi game da wannan kalma.

     

    Daga ciki akwai Hassan (1998:94) ya nuna cewa, bayan al’ummar Kano sun rungumi wannan rana ne ta takutaha, sai Maguzawa da suke gabatar da bukukuwansu na bauta a lokacin suka damu, wasu suka bar garin zuwa qauyuka, suna cewa, “wannan sallar taku-ta ba tamu ba ce”. Daga nan sai aka sami kalmar takutaha.

     

    Wasu kuwa suna ganin Kalmar ta samu ne daga qaulin Shehu Usmanu Danfodiyo, a lokacin da almajiransa suka yiyo bara a ranar da shekarar da aka haifi Annabi salallahu alaihi wasallam ta kewayo, amma sai ya qi daukar komai a ciki, ya ce, “ ai wannan taku ta”. Daga nan sai aka sami kalmar “takutaha”.

     

    Wasu kuma suna ganin ma’anar Kalmar takutaha ita ce, “Allah ya maimaita mana”, wasu kuma sun ce sunan Ma’aiki ne. Haka nan, wasu suna ganin Kalmar ta samu ne daga sunan wata baiwar Allah mai suna Taku, ‘yar Malam Usman Attuman, babban waliyin nan da ya zauna a Madabo.

     

    A dunqule, za a iya cewa bikin takutaha yana daya daga cikin bukukuwan addini da ake yin sa a birnin Kano, duk ranar 19 ga watan Rabi’ul awwal, wato watan da aka haifi Annabi Muhammadu salallahu alaihi wasallam kuma dai-dai da ranar sunan sa.

Back to top button