AN GUDANAR DA GAGARUMIN TARON BIKIN MAULUDIN MANZON ALLAH SAW A GOMBE
Daga: Babangida A. Maina
An gudanar da gagarumin bikin Mauludin Annabi Muhammadu SAW a gidan Alh Ibrahim Sufi dake anguwan Danaje cikin birnin Gombe.
Taron Mauludin wanda aka saba gabatar duk shekara inda manyan baki daga sassa daban-daban na fadin Najeriya suke gabatar da kasidu da lakcoci akan tarihi na Manzon Allah SAW da halayen sada dabi’un sa.
An gabatar da takarda mai taken koyi da kyawawan dabiu na Manzon Allah SAW wanda Sheikh Nuhu Abdulwadud ya gabatar da wasu daga cikin mahalarta taro.
Hon Muhammadu Magaji Gettado kwamishina wanda ya wakilci gwamnan jihar Gombe Alh Muhammad Inuwa ya bayyana halaye na bayin Allah waliyai a matsayin abun koyi tare da godiya daga gwamnan jihar Gombe.
Hon, kwamishinan matasa na jihar Gombe yayi kira ga dukkan matasa da suyi koyi da kyawawan halayen da dabi’u irin na Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu ﷺ a kowanne hali na rayuwar su. Inda ya godewa duk wanda ya samu halartan taro Mauludin Manzon Allah SAW.
Daga karshe Sallaman Gombe ya bayyana sakon mai martaba sarkin Gombe a taron Mauludin, an gabatar da jawabai mabanbanta daga wurin malamai da zikirin da yabon fiyayyen halitta Manzon Allah SAW.
Sheikh Ibrahim Sufi wanda shine mai masaukin baki ya bayyana godiya ga Allah da masoya Manzon Allah SAW bisa halartan taro Mauludin Allah ya maimaita mana.
Allah ya Maimaita Mana Ya Kara Mana Soyayyan Annabi Muhammadu ﷺ Ya Sakawa Wadannan Bayin Allah Da Alkhairi. Amiin