Takaitaccen Tarihin Goni Sayyadi Mahir Abdulrahman Nguru Mai Diwani (1983-2023).
An Haifi SAYYIDI MAHIRU MAI DIWANI a Cikin Garin NGURU(Jihar Yobe) Tsatso (Ɗa) Ne Ga Babban Sahabin/Almajirin MAULANA SHEHU MUHAMMADU NGIBRIMA (R.A) Wato SHEIKH MUHAMMADU KIME(R.A).
SAYYIDI Yayi Karatun Al-Qur’ani Tsangaya a Garin GEIDAM a Zawiyyar Sheikh Ainoma(Anan Ya Samu Al-Qur’ani),
Daga Bisa Ni Ya Tafi Birnin MAIDUGURI a Ci Gaba Da Neman Ilimi, Anan Ne Ma Ya Haɗu Da Shahararren Makarancin Diwanin Nan Wato SHEIKH JIBRIL ADDAIF, Inda Ya Zauna a Karƙashinsa Na Wani Lokaci.
SAYYIDI Daga Karshe Ya Dawo Gida(Nguru) Yayin Da Mutan Gari Suka Fara Farga Da Baiwar Da SAYYIDI Ya Dawo Da Ita, Sai Aka Yi Ta Kai Masa Caffa, Gayyata Ta Ko Ina(Ya Zo Ya Rera Diwani), Cikin Ƙanƙanin Lokaci Muryar Diwanin Sayyidi Ta Karaɗe Ko Ina.
SAYYIDI Ya Samu Tafiya Birnin KAOLACK (Senegal) a Shekarar 2019, Inda Ya Ziyarci MAULANMU SHEHU IBRAHIM NIASSE(R.A), Kuma Ya Karanta Diwanin SHEHU(R.A) a Gaban AHLIN SHEHUN(R.A).
SAYYIDI Yayi Wafati Ya Bar Yara Bakwai(07).
Muna Addu’ar ALLAH(S.W.T) Ya Kiyaye Bayansa, Ya Albarkaci Abin Da Ya Bari.
ALLAH Ya Ƙara Haskaka Makwancin SAYYIDI, Ya Ƙara Masa Kusanci Da SHUGABA(S.A.W).
Muma ALLAH Ya Kyauta Namu Ƙarshen Don Albarkar SAYYIDUL-WARA(S.A.W). Amiin Yaa ALLAH.
Daga: Othman Muhammad