RASUWA

  • Allah Ya Yiwa Matar Sayyadi Ali Dahiru Bauchi RA Sayyada Hajiya Asabe Rasuwa A Bauchi.

    Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un 😭😭

     

    …Allah Ya Yiwa Matar Sayyadi Ali Dahiru Bauchi RA Sayyada Hajiya Asabe Rasuwa A Bauchi.

     

    Marigayiya Sayyada Hajiya Asabe wanda Allah ya karbi rayuwar ta mata ce ga dan Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR wato Sayyadi Ali Cisse Sheikh Dahiru Bauchi RA.

     

    Sayyada Asabe mahaifin ta shine Alh Ali Auta ma’adakin Lokoja. ta rasu ta bar yara da dana da kuma mahaddata Alkur’ani ur’ani mai girma.

     

    Muna mika ta’aziyya ga Maulana Sheikh Dahiru Bauchi RA da kuma Sayyadi Ali Dahiru Bauchi bisa rasuwan mai dakin (Mata) Sayyadi Ali Sayyada Hajiya Asabe wanda Allah ya karbi rayuwar ta a daren jiya Asabar 5/11/2022.

     

    Za’ayi jana’izan ta a zawiyyan Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA dake titin Bauchi zuwa Gombe cikin garin Bauchi. Da misalin karfe hudu da rabi na yamma 4:30

     

    Babangida A. Maina

    Tijjaniyya Media News

  • INNA’LILLAH: Allah Ya Karbi Rayuwar Sheikh Salihu Umar Malalayel Gombe

    INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN😭

     

    Allah ya yiwa Sheikh Salihu Umar Malalayel rasuwa, Malami masanin ilimoma wanda ya ƙarar da rayuwarsa cikin hidimar Addini da al’umma. Yayi fama da jinya kafin rasuwarsa.

     

    Za ayi jana’izarsa gobe Alhamis ƙarfe 3:00pm na yamma a Zawiyyar Maulana Shehu Gajali dake Tudun Wadan Pantami Gombe, Gombe State.

     

    Allah ya gafarta masa ya sada shi da Annabin rahama Sallallahu Alaihi Wasallam. Amiin

     

    Mustapha Abubakar Kwaro

    Tijjaniyya Media News

  • Shahararren Malamin Muslunci A Masar Sheikh Yusuf Ya Rasu.

    Innalillahi Wa’inna Ilahir Raji’un 😭😭

     

    Shahararren malamin addinin Musulunci, Youssef al- Qaradawi wanda ke cikin kusoshin kungiyar Muslim Brotherhood ya rasu.

     

    Sheikh Youssef bawan Allah wanda ya sadaukar da rayuwar sa wurin hidimtawa addinin Islama kuma tsohon shugaban kungiyar kuma babban limaman Musulunci a duniya ya rasu ne yana da shekaru 96.

     

    An haife shi a Masar kafin ya koma Qatar da zama, Youssef al- Qaradawi ya wallafa litattafan musulunci da dama.

     

    Yana gabatar da shirin talabijin a tasha al-Jazeera kuma miliyoyin mutane ne ke bin wa’azinsa a fadin duniya.

     

    Muna addu’an Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa. Amiin Yaa Allah.

  • Allah ya yiwa sarkin malaman Zuru Sheikh Abdulrahman Hamza Balarabe rasuwa.

    INNA’LILLAH WA’INNA ILAIHIR RAJI’UN

     

    …Allah ya yiwa sarkin malaman Zuru Sheikh Abdulrahman Hamza Balarabe rasuwa.

     

    Allah ya yiwa babban malamin musulunci kuma shehun Darikar Tijjaniyya a Najeriya Sheikh Abdulrahman Hamza Balarabe Zuru dake Jihar Kebbi a arewacin Najeriya rasuwa,

     

    Shehin malamin ya bada gagarumar gudunmuwa a addinin Islama a Najeriya ya kasance mutum mai tawali’u da tsaron Allah tausayi da kuma taimakon addinin Allah,

     

    Allah ya jikansa da rahama ya kyautata tamu bayan tasu alfarmar Al’qur’ani. Amiin

     

    Daga Abbakar Aleeyu Anache

  • Janaza Mafi Girma a Tarihin Ƙasar Pakistan Masa Da Mutane Miliyan Biyar Ne Suka Halarci Sallar Jana’izan.

    “Janaza Mafi Girma a Tarihin Ƙasar Pakistan”

     

    Wata mata a kasar Pakistan tayi batanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam, aka kulleta a kurkuku kafin yanke mata hukunci, sai Gwamnan jihar Punjab ƙasar wanda yake samun goyon bayan Amurka yai ta ƙoƙarin kubutar da matar ta hanyar canja hukuncin da ƙasar ta tanada ga duk wanda ya munana ladabi ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam.

     

    Matakin da Gwamnan jihar Punjab ya dauka bai yiwa mai tsaron lafiyarsa dadi ba, sai ya dauki bindigarsa ya harbi Minister harbi sama da 20 ya kashe shi har lahira.

     

    Hukumomin ƙasar suka kama mai tsaron lafiyar Gwamnan mai suna “Muttaz Qadri” aka yanke masa hukuncin kisa, bayan aiwatar da kisan aka miƙa gawar Muttaz ga danginsa.

     

    Mutanen Pakistan sun fito jana’izar wannan gwarzo wanda ya fansar da ransa ga masoyin mu Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Sallam, wadannan sune kadan daga cikin hotunan jana’izar fiye da mutum miliyan 5 suka halarci jana’izar wanda ya hada da sojoji da ‘yan sandan kasar.

     

    Tabbas abinda Muttaz Qadri yayi shi ake kira so! Allah ya jaddada masa rahama, Allah ya kara kusantamu Annabi Muhammadu SAW. Amiin

     

    Daga: Sadi Ahmad Yalo.

Back to top button