RASUWA

  • Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un, Allah ya yiwa Sayyadi Ja’afar Sa’eed Attijjany Al’faidiy rasuwa.

    Innalillahi wa inna ilaihirraji,un 😭😭

     

    Allah ya yiwa Sayyadi Ja’afar Sa’eed Attijjany Al’faidiy rasuwa wanda dan’uwa ne na hakika cikin tafiyan faidah.

     

    Sayyadi Ja’afar Sa’eed Attijjany Al’faidiy dan uwan mu batijjane ne kuma masoyin nanzon Allah SAW ne na hakika.

     

    Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa Allah ya karbi shahadar sa. Amiin

     

    Babangida Maina

  • Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un Allah Ya Yiwa Babban Malamin Sheikh Habib Abubukar Adnan Rasuwa.

    Innalillahi wa inna ilaihi raji’un 😭😭

     

    Babban malamin Musulunci a duniya ya rasu a kasar Jordan Sheik Habib Abubukar Adnan.

     

    Babban abin bakin-ciki nake sanar daku rasuwan babban malamin a wannan zamanin namu a fagen ilimin fiyayyen halitta da zamantakewa ta mahangar Musulunci (‘ilm ul-Ākhir al-Zamān), Habib Abubakar al-‘Adanī, ya rasu, dake jihar amman a kasar Jordan.

     

    Allah ya jaddada masa rahma ya gafarta masa, Allah ya kara kusanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu ﷺ.

     

    Allah ya tashe shi tare damu da shugaban mu Sayyiduna Muhammad (SAW) a cikin mafi daukakar Aljannah. Amiin

     

    Daga: Babangida A. Maina

    Founder CEO Tijjaniyya Media News

  • Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un Tijjanawa Na Jimamin Rashin Wani Matashin Dan Uwan Su

    SAYYADI ƊAHIRU YAYI DACE DUNIYA DA LAHIRA.

     

    ALLAH ya yiwa Sayyadi Dahir Abubukar DK dake karamar hukumar Dukku jihar Gombe rasuwa.

     

    Irin wannan ƙarshe muke roƙo kullum, Allah ya bamu ikon cikawa da imani, kafin nan kuma ya albarkacemu da aikata aikin alkhairin da za’a tunamu dashi bayan macewarmu.

     

    Wannan bawan Allah batijjanene ɗan uwana kuma ɗan faira na gaskiya ba shirme ba. Ban taɓa wata mu’amala dashi ba ko a Media sai dai sau tari mukanyi musafaha sakamakon haɗuwa cikin hidimar Allah.

     

    Yau mun wayi gari ya koma ga Allah, tun safe kyakkyawar shaida kawai nake gani ake masa musamman ta soyayyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.

     

    Shi kam yayi dace, muma Allah yasa mu dace mu ciki da imani Albarkacin Shugaban Halitta Sallallahu Alaihi Wasallam. Amiiin

     

    Mustapha Abubakar Kwaro

    19/07/2022

  • Dubban Al’umma Musulmi Ne Suka Halarci Sallar Jana’iza Sayyadi Zakiru Yahya Ahlul Baiti A Lafia.

    JANA’IZA CIKIN HOTUNA:

     

    Yadda Aka Gudanar Da Sallar Jana’izan Dan’uwan Mu Musulmi Zakiru Yahya Ahlul Baiti A Yau Talata 19/07/2023.

     

    Dandazon Al’umma Musulmi Kenan Wanda Suka Halarci Sallar Jana’iza Sayyadi Zakiru Alhul Bait (Sakataren Hilaqul Zikirullah Na Jihar Nasarawa) Dake Birnin Lafia A Jihar Nasarawa

     

    ALLAH Ya Jaddada Masa Rahma Ya Gafarta Masa Allah Ya Karbi Bakwancin Sa. Amiin

     

    Babangida A. Maina

  • Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un Allah Ya Yiwa Zakiru Yahya Ahlul Baiti Dake Lafia Rasuwa.

    INNA LILLAHI…

     

    ALLAH Ya Yiwa ZAKIRU YAHYA AHLUL-BAITI LAFIA Rasuwa Jiya Da Daddare, Hakika An Yi Babban Gi6i a Hidimar MANZON ALLAH (S.A.W) Da ZAKIRAI a ‘Kasar LAFIA, Hadimi Na Gasken-Gaske.

     

    Za’a Yi Jana’izarsa Yau Da Misalin ‘Karfe 02:00 (Bayan Sallar Azahar) a Unguwar Rimi Uku Lafia, Jihar Nasarawa.

     

    A Madadin Hukumar Gudanar Wa A Kamfani Tijjaniyya Media News Karkashin Jagoranci Babangida A Maina Tana Mika Sakon Ta’aziyya Ga Yan’uwa Da Iyalan Mamacin Allah Ya Bada Hakurin Wannan Rashi.

     

    ALLAH Ya Jaddada Rahma a Gare Shi, Ya ‘Kara Masa Kusanci Ga SHUGABA (S.A.W), In Namu Lokacin Yayi, ALLAH Ya Kyautata Namu ‘Karshen, Ameeeeeen

     

    Daga: Othman Muhammad

     

     

Back to top button