Duniyar Musulunci Tayi Babban Rashin.
Allah ya yiwa mai gadin kabarin Manzon Allah SAW, Agha Habeeb Muhammad al-Afari, rasuwa a yau Laraba. Wanda yana daya daga cikin manya-manyan tsofaffin masu gadi a Masallacin.
Za’ayi gusanar sallar jana’izarsa bayan Magriba yau a Masallacin Haramin Makkah.
Muna Addu’an Allah Ya Jaddada Masa Rahma Ya Gafarta Masa Allah Ya Hadashi Da Manzon Rahma Annabi Muhammadu ﷺ. Amiiin
Daga: Shafin Haramain