Kimanin Mutane Miliyan Uku (3M) Suka Halarci Mauludi Manzon Allah SAW A Garin Bauchi.A Bauchi

Dandazon Al’umma Kenan A Wajen Taron Mauludin Manzon Allah SAW A Jihar Bauchi dake arewacin Najeriya.

 

Rahotanni daga jihar Bauchi dake arewacin Najeriya sun tabbatar mana da cewa a kalla mutane sama da miliyan uku ne suka halarci taron Mauludin Manzon Allah SAW wanda ka gudanar a jihar Bauchi a daren Asabar kamar yanda aka saba.

 

Taron Mauludi wanda ake yi duk shekara karkashin jagorancin babban malamin addinin Musulunci kuma shehin Darikar Tijjaniyya a duniya Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR ya samu gudanar kamar yanda aka saba duk shekara a filin wasa na Abubakar T/B dake garin na Bauchi.

 

An fara gudanar da taron da bikin saukar yaye dalibi mahaddata Alkur’ani mai girma daga bisani aka yi wazifa sai an yi babban taron Mauludi wanda mutane suka halarta daga sassan fadin Najeriya dama fadin duniya.

 

An gabatar da tarihin fiyayyen halitta Annabi ﷺ da wasu daga cikin rayuwar sa daga malamai da shehunai, da karance-karance na wakokin yabon Annabi SAW.

 

Cikin wadanda suka samu halarta akwai mataimakin gwamnan jiha, sarakunan gargajiya, Malamai da sauran mutane, daga karshe an gabatar da addu’o’i don samun zaman lafiya a Najeriya.

 

Allah ya maimata mana. Amiiiin Yaa ALLAH

 

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button